✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan jami’o’i sun bi sahu a yajin aiki

Ma’aikatan jami’o’i sun fara yakin aiki domin matsa wa gwamnati lamba ta biya musu bukatunsu. Yajin aikin na kwana 14 na zuwa ne a daidai…

Ma’aikatan jami’o’i sun fara yakin aiki domin matsa wa gwamnati lamba ta biya musu bukatunsu.

Yajin aikin na kwana 14 na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shirye bude jami’o’i domin ci gaba da darussa.

Kungiyoyin manyan  ma’aikata da wadanda ba malaman jami’o’i ba (SSANU da NASUU) sun fara yajin aikin ne daga Litinin 5 ga Oktoba, 2020.

Ma’aikatan na zargin bambance-bambance a tsarin albashin bai-daya (IPPIS) da kuma rashin biyan su alawus-alawus dinsu.

Shugaban SSANU, Kwmaret Samson Ugokwe, ya kuma zargin malaman jami’o’i da kwace shugabancin bangarorin da ba na koyarwa ba.

Ya ce yin hakan  “ya saba ƙarara da tsarin aiki da kuma dokokin da suka kafa bangarorin”.

Sauran bukatun sun hada da biyan su alawus-alawus din da ma’aikatan suka cancanta da kuma magance almundahana a jami’o’i.