✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Janar AbdulSalami ya shawarci ’yan siyasa su rika martaba ’yancin jama’a

Tsohon Shugaban kasa Janar AbdulSalami Alhaji Abubakar ya shawarci ’yan siyasa su rika martaba ’yancin jama’a na zaben shugabannin da suke so tare da cika…

Tsohon Shugaban kasa Janar AbdulSalami Alhaji Abubakar ya shawarci ’yan siyasa su rika martaba ’yancin jama’a na zaben shugabannin da suke so tare da cika alkawuran da suka yi a idan suna so su ci gaba da yin tasiri a yankunansu.
Janar AbdulSalami Abubakar ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa dk manema labarai a Minna, inda ya ce ko shakka babu Najeriya na samun ci gaba a fannoni daban-daban daga lokacin da aka sake dora ta a turbar mulkin dimokuradiyya a1999.
Janar AbdulSalami ya ce duk da ci gaban da aka samu a tsawon wannan lokaci, akwai sauran jan aiki a gaban ’yan siyasa da ’yan Najeriya ya kamata su mayar da hankali a kai.Ya ce ya dace su rika tuntubar jama’a game da al’amuran da suka zabe su, kuma a rika gudanar da ayyukan da ake ganin ya dace da su.
Tsohon Shugaban kasar ya ce ’yan siyasa su san cewa ba illa ba ne jama’a sun kasance suna da bambancin ra’ayin siyasa domin duk da wadannan bambance-bambance, manufarsu guda ce ita ce ta gina wannan kasa da Allah Ya yi wa arzikin jama’a da albarkatun kasa.
Da ya juya kan yadda jama’a suka karkata a kan dole sai wasu jama’a sun fito takarar zaben shekarar 2015, Janar AbdulSalami Abubakar ya nemi su sake nazari a kan wadannan jama’a da suke zawarcin tsayawa takara a madafun mulki a kowace jam’iyya mutum ya samu kansa, don kuwa ba za a karkata wuri daya domin tafiya daya ba, dole ne a samu bambancin ra’ayi a siyasance.
Ya yaba gudunmawa da sadaukarwar da ’yan jarida suka bayar wurin ganin an samu nasarori da wannan kasar ta samu.Ya kuma nemi su ci gaba da bayar da gudunmawar bunkasar fannonin da suka shafi jama’a baki daya.