✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Janye tallafi: kungiyar kwadago za ta sa zare da gwamnati

Ga dukkan alamu janye tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta sanar a shekaranjiya Laraba zai farfado da gagarumar zanga-zangar nan ta shekarar 2012 mai…

Ga dukkan alamu janye tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta sanar a shekaranjiya Laraba zai farfado da gagarumar zanga-zangar nan ta shekarar 2012 mai taken #occupyNigeria inda haka na iya sanya zare a tsakanin gwamnatin da kungiyoyin kwadako da na kare hakkin jama’a.
Tuni kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta ce, ba ta yarda da karin kudin man fetur din ba bayan da Gwamnatin Tarayya ta ce ta cire tallafin mai, inda za a sayar da lita daya ta man fetur a kan Naira 145.
Sakataren Watsa Labarai na kungiyar NLC, Kwamared Nuhu Abbayo Toro ya ce, ba za su amince da karin farashin man fetur ba, kuma kungiyar NLC, za ta dauki mataki kan karin kudin man nan gaba bayan wani taro da za ta gudanar.
Tuni wadansu ’yan Najeriya suka fara jawo ra’ayin ’yan Najeriya a shafukan sadarwar zamani domin fitowa gagarumar zanga-zanga, kuma kungiyar Manyan Ma’aikata ta kasa (TUC) ta bayyana karin kudin man a matsayin wani juyin mulki ga kungiyoyin ma’aikata.
Shugaban kungiyar TUC, Mista Bobboi Kaigama, da Mukaddashin Babban Sakataren kungiyar Mista Simeso Amachree, sun ce sun halarci zaman da aka yi ranar Larabar amma an yi musu dungu ne a kai/ Sun ce ba su san yadda aka yi gwamnati ta yanke shawarar sanya sabon farashin ba ko shawarar da ta yanke na barin ’yan kasuwa su yanke shawara kan kudin man ba.
 kungiyar TUC ta ce za ta yi zaman gaggawa a yau Juma’a domin tattauna sanarwar ta gwamnati tare da daukar matakin da zai kasance mafi alfanu ga ma’aikatan Najeriya da kuma talakawa.
Tuni kungiyar Dillalan Man fetur Masu Zaman Kansu ta Najeriya (IPMAN) ta yi maraba da karin kudin man, inda Mataimakin Shugaban kungiyar Alhaji Abubakar Maigandi, ya fadi a shekaranjiya Laraba a Abuja cewa, shawarar za ta taimaka wajen kawo karshen wahalar man a kasar nan. “Wannan labara ne mai dadi; abu mafi kyau a janye tallafin mai gaba daya a bar kasuwa a bude ta yadda mutane za su yanke hukunci kan yadda za su sayar da man bayan sun shigo da shi,” inji shi.
’Yan Najeriya na ci gaba da sukar gwamnatin Shugaba Buhari kan yadda ya ba su kunya wajen kara kudin man, bayan a lokacin kamfe Jam’iyyar APC ta Shugaba Buhari ta sha nanata cewa babu wani mai suna tallafin mai.
Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose na cikin wadanda suka la’anci karin kudin man,inda ya bayyana hakan da rashin tausayi da kiyayyar da gwamnatin Buhari ke nuna wa ’yan Najeriya. Ya ce kara kudin mai da fiye da kashi 70 cikin 100 ya sake tabbatar da hasashensa na wahalar da za a shiga a bana, inda ya yi zargin cewa an kirkiro wahalar man fetur ne da gangan domin a share hanyar kara kudin man.
Minista a Ma’aikatar Man Fetur Mista Ibe Kachikwu, wanda yak are karin kudin man daga Naira 86.50 zuwa 145 ya ce hakan ne kawai zai raba jama’a da sayen man a Naira 150 zuwa 250 da suke ciki a kasuwar bayan fage.
Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinabjo ne ya jagorancin zaman da aka yanke hukuncin kara kudin mai din zaman day a samu halartar shugabannin kungiyar gwamnoni da na majalisa da na kwadago da na ma’aikatan mai wato (NLC, TUC, NUPENG, da PENGASSAN).