✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Japan na so a ba Afirka kujerar dindindin a Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya

Japan ta ce rashin adalci ne a hana Afirka wakilci a Kwamitin

Kasar Japan za ta matsa lambar ganin an samar wa da nahiyar Afirka kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaban Kasar, Fumio Kishida, ne ya fadi haka a wani taron tattaunawa kan ci gaban nahiyar Afirka da ake yi a birnin Tunis a ranar Lahadi.

Mista Kishida ya jaddada kudurinsa na ganin an gyara abin da ya kira rashin aldalci ga nahiyar, ta hanyar kin samar mata da kujera ta dindindin a Kwamitin Tsaron.

“Domin Majalisar Dinkin Duniya ta yi aikinta yadda ya kamata don samar da zaman lafiya, akwai bukata ta gaggawa na karfafar Majalisar da sauye-sauye na bai-daya a Kwamitin Tsaron,” inji Kishida.

A watan Yuni ne Japan ta zama cikon kasashe biyar da aka zaba da su zama mambobi a Kwamitin na wucin-gadi daga shekarar 2023 zuwa 2024.

Kwamitin dai na da mambobi 15. Biyar daga cikinsu na da kujerar ta dindindin kuma suna da ikon hawa kujerar-na-ki.

Wadannen kasashe su ne Birtaniya da Rasha da China da Faransa da kuma Amurka,

Sauran kujeru 10 kuma ragowar kasashen duniya ne ke hawa na tsawon shekara biyu. Biyu daga cikinsu kuwa ana sanar da su ne a kowacce shekara.