✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarabawar aljani

Wasu mutum uku ne suke tafiya a jirgin ruwa, da Baturen Amurka da na Jamus da kuma dan Najeriya. Kwatsam sai ga aljani ya bayyana…

Wasu mutum uku ne suke tafiya a jirgin ruwa, da Baturen Amurka da na Jamus da kuma dan Najeriya. Kwatsam sai ga aljani ya bayyana a jirgin kuma ya ce zai kashe su idan ba su cika ka’idojin da zai shimfida musu ba. Aljani ya ce: “Idan kowane daga cikinku yana son ya tsira da ransa to tilas ne ya jefa wani abu a cikin kogi kuma ya kasance abin da za ku jefa wanda ni ba zan iya daukowa ko gani ba ne.” Nan take Baturen Amurka ya mamaye shi ya jefa makallin rigarsa a cikin kogi. Aljani ya bi shi kuma ya ciro, sai ya kashe shi.  Shi kuma Baturen Jamus sai ya jefa allura cikin ruwa, nan ma aljani ya bi ya dauko kuma ya kashe shi. Da aka zo kan dan Najeriya sai ya kalle ledar ruwan fiyawota da ke hannunsa, ya zuba ruwan cikin kogin ba tare da ledar ba, ya ce wa aljani: “To ina so ka debo mani daidai ruwan da na zuba a kogin in da gaske kake.” Nan fa idon aljani ya raina fata kuma dan Najeriya ya tsira.
Daga Ahmad Garba Muhammed 08028797883