✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Legas ta samar da wutar lantarki mai zaman kanta ga sakatariyar jihar

A wani yunkuri na wadata Jihar Legas da wutar lantarki gwamnatin jihar ta kafa kamfanin lantarki mai karfin megawat 10.6 da zai samar da wuta…

A wani yunkuri na wadata Jihar Legas da wutar lantarki gwamnatin jihar ta kafa kamfanin lantarki mai karfin megawat 10.6 da zai samar da wuta ga sakatariyar jihar da Titin Awolowo da Kasuwar Ikeja.

Da yake jawabi a wurin bude kamfanin, Gwamna Babatunde Raji Fashola ya ce gwamnatin na fatan wutar za ta taimaka ga tsaron dukiyar jama’a ta yadda miyagu ba za su samu damar aikata ayyukan assha ba. Ya ce irin wannan kamfani ne gwamnatin ta samar a Titin Carter, kuma yana taimaka wa jama’ar yankin kwarai da gaske.
Gwamnan ya ce gwamnatin ta samar da irinsa a tituna 11 da ke Alimosho, sai dai ya ce babban abin farin cikin shi ne komai da aka hada wajen kafa kamfanin wutar lantarkin an samar da su ne a nan cikin gida Najeriya.
Gwamna Fashola ya ce baya ga sakatariyar, gwamnati za ta samar wa makarantu da asibitoci da kotuna da manyan tituna wutar lantarki ta yadda ba sai sun jira wuta daga kamfanin wutar lantarki na kasa ba.
Gwamnan ya ce gwamnatin za ta ci gaba da samar wa al’ummar jihar abubuwan inganta rayuwarsu, kamar wutar lantarki da asibitoci da tituna da makarantu.
Ya ce tun daga lokacin da gwamnati ta gane cewa samar da wutar lantarki da kanta ya fi sauki, ya sa daga yanzu duk manyan wurare mallakar gwamnati za su samar musu da wutar lantarkinsa mai zaman kansa, inda ya ba da misali da wutar lantarki na gwamnati na ba da megawati 12.7 a kowane awa daya, amma na gwamnatin jiha na samar da ninkin haka sau biyu zuwa uku.
Gwamna Fashola ya shawarci magina da masu tsara taswirar gine-gine su samar da tsarin gini da bai bukatar amfani da janareta ko wutar lantarki da rana ko ginin da ba ya bukatar fanka a kowane lokaci.
Kwamishinan Wutar Lantarki da Albarkatun kasa na Jihar Injiniya Taofeek Tijjani ya ce samar da wutar lantakin mai zaman kansa zai taimaka wajen inganta ayyukan sakatariyar da habaka tattalin arzikin jihar. Ya ce an samar da wutar lantarki ne da hadin gwiwar kamfanin mai na Oando da bankin Fidelity.