✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Nasarawa ta bai wa ’yan gudun hijira tallafin kayayyakin miliyoyin Naira

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bai wa ’yan gudun hijirar da ke da rigirgimun kabilanci ya shafa kwanakin baya a jihar tallafin kayayyakin agaji na miliyoyin…

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bai wa ’yan gudun hijirar da ke da rigirgimun kabilanci ya shafa kwanakin baya a jihar tallafin kayayyakin agaji na miliyoyin Naira.
A jawabinsa a wajen mika kayayyakin ga ’yan gudun hijira a gidan gwamnati da ke Lafiya, Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura ya ce gwamnati ta dauki matakin ne don rage wa ’yan gudun hijirar wahalhalun da suke fuskanta a halin yanzu sakamakon rashin dukiyarsu a lokutan fadace-fadacen kabilance a wasu kauyukan jihar kwanakin baya.
Gwamna Al-Makura ya ce wannan ba shi ne karo na farko da gwamnatinsa ta bai wa ’yan gudun hijirar tallafi ba kuma a cewarsa za a ci gaba ta yin haka. Ya kara da cewa batun rigirgimun kabilanci a jihar ya fara zama tarihi sakamakon kwararan matakai da gwamnatinsa ta dauka don kawo karshen rigirgimun musamman ta hanyar sulhunta kabilun jihar.
Gwamna Al-Makura ya shawarci wadanda suka amfana da tallafin su yi kyakkyawan amfani da su kuma su guji sayar da su.
Kayayyakin da aka bai wa ’yan gudun hijirar sun hada da katifu da tabarmi da buhunhunan shinkafa da sabulai da katan-katan na Maggi da zannuwa da suturun yara da kuma tsabar kudi Naira miliyan 27 da sauransu.
Sarkin Lafiya kuma Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Alhaji Isah Mustapha Akwai ya jinjina wa Gwamnan a madadin wadanda suka amfana da tallafin inda ya ce babu shakka tallafin zai rage wa ’yan gudun hijirar matsaloli da dama da suke fuskanta.
Aminiya ta gano ’yan gudun hijirar sun fito ne daga kauyukan da suka hada da Assakio da Adogi da Gidan-Buba da Injila da Fadaman-bauna da Kwandare da Bakin-Rijiya da Shabu da Uggah da Basa da Udege-Magaji da Obi da sauransu.