✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Neja a doron shekara 40

Jihar Neja a doron shekara 40 Editan Aminiya ba ni dama in yi tsokaci a kan Jihar Neja a doron shekara 40; a kwana a…

Jihar Neja a doron shekara 40

Editan Aminiya ba ni dama in yi tsokaci a kan Jihar Neja a doron shekara 40; a kwana a tashi babu wuya a wurin Allah. Shekaru 40 ke nan da Jihar Neja da ke Arewacin Najeriya ta zama ‘yantattar jihar (da samun ’yanci).Ta kuma samu ’yan’tuwar ne daga hannun Shugaban kasa na wancan lokacin Janar Murtala Ramat Muhammad da ya cirota daga Jihar Sokoto a shekarar 1976 inda Riyal Adiral Murtala Nyako ya zama gwamnan ta na farko. Jihar Nejar dai zuwa yanzu ta yi gwamnoni har 14, inda sojoji tara (9) suka mulke ta.Yayin da farar hula biyar(5) suka ja akalar ta. Da fatan Allah Ubangiji ya kara maimaita wa Jihar Neja wasu shekaru masu dimbin yawa da albarka. Haka ina fatan shugabannin jihar na yanzu za su kara kaimi sosai wajen kawo abubuwan ci gaban jihar da al’umma baki daya.Allah ya kara wa Jihar Neja albarka da daukaka da Najeriya baki daya.
Daga Haruna Muhammad Katsina. Shugaban kungiyar Muryar Jama’a. 07039205659 ko 07057491050 [email protected]

Haba Aminiya !

Editan Aminiya a gaskiya mutane suna yawan korafi a kan jiridarku a wajen filin wasiku duk da dai ba komai ake ba ku ba, amma al’ummar Apapa da ke Legas a gaskiya sun koka a kan kin sako musu sakonninsu. Kuma a duk Legas, Apapa ce ta biyu wajen sayen Aminiya. To  don.Allah in da hali ku gyara. Daga Yahaya Ahmed Jabo Apapa, Legas 08128286038.
Aminiya ba ku kyauta ba

Yanzu Aminiya ba ku kyauta mana ba, mu  ’yan media Jihar Kano. Sau uku muka rubuta muku sakon ta’aziyar dan uwanku dan jarida, Alhaji Sule Magagi Beli, ba ku buga ba. Za mu juya muku baya. Daga Salisu Maliya Gwauron Dutse, karamar Hukumar Dala, Jihar Kano 08099139741.
Shawara ga Aminiya

Salam. Mun ji dadi da kuka turo mana kalandar sabuwar shekara ta Turawa, to yana da kyau idan Allah Ya kai mu shekara mai zuwa muma ta Musulunci a turo mana ita.Daga Aliyu Umar Master Sarina Abu Khamis
Kukanmu ga Gwamna Masari

Edita bayan gaisuwa mai yawa da fatan alkhairi, Allah ya sa haka amin. Bayan  haka  ina so a ba ni dama domin in mika kukan mutanen Daura ga  Gwamnan  Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, muna rokon maigirma don Allah a taimake mu a gyara mana mayankar dabbobi ta Daura, saboda ba mu da isasshen ruwa kuma mayankar ba ta da rufi ga plastar kasa, inda muke aikin nama. Duk ta lalace. Don haka muna roko gareka ya maigirma gwamna, a gyara mana muma a yi mana irin ta zamani, babu abin da ya fi ci mana tuwo a kwaryakamar wannan rashin rufi. Muna fatan Allah ya ba ka ikon yi amin  08148442241   08085127726. Daga Hadi Tsohon Sarki Daura
Addu’a ga Aminiya

Salam Edita. Yau jinjina da yabo tare da addu’a. Na zo in yi wa gidan jaridarmu ta Aminiya Allah ya kara muku daukaka da hazaka. Assalam, Gaba Dai Gaba Dai Aminiya Allah ya kara taya ku riko da daukaka Amin. Daga Muhammad Ahmad Idris a Kabuga Kano daAbubakar Plumber 07039508352.
A sa ido a kamfanin wutar lantarki

Assalam Aminiya don Allah a taimake mu, a shaida wa Maigirma Shugaban kasar mu, Muhammadu Buhari a hanzarta a yi wani abu kan NEPA, wato ma’aikatar wutar lantarki, don sun fi ’yan sanda cin hanci da rashawa. Abin  na su ya kai intaha. Daga Isah Dilwaala Abuja 0805 904 4449  
 Shugaban kasan ka rage yawo

Assalamu Alaykum. Edita ka ba ni dama in yi kira da shugaban kasa da mataimakinsa a kan su ji tsoron Allah su  daina yawuce-yawuce zuwa kasashen waje, su tsaya su yi wa al’umma aiki. Ga matsaloli sun dabaibaye Najeriya.
Daga Nura Umar Zagga 08060817110
Addu’a ga Gwamna Yahaya Bello  

Allah ya tayaka rikon amana, Allah ya ba ka masu baka shawara nagari  akan  mulkin ka amin.  Allah ya kareka daga makiya amin.  Ana ganin ko ba ka taba yin gwamna ba,  yau ga shi Allah  ya ba ka wanan dama.  Na farko gareka,  shi ne,  hakuri da jama’a  Allah ya taya ka riko. Amin.  Daga Yusuf  Buzu  Sakkwato  07033412184
Tambaya  ga Gwamnatin Kano

Salam. Zuwa ga Edita. Tambaya  ga Gwamnatin Kano wai barayin shanu da aka yi wa afuwa dama haka doka ta tanada in an kama mai laifi a kyale shi? Daga dan Bashir Madatai 08103135352.
Taya murna ga jami’ar ABU

Edita ba ni fili in taya Jami’ar Ahmadu Bello, ABU Zariya murna kan  bikin da ta yi na yaye dalibai  karo na 38. Allah Ya jikan Gamji, Allah Ya kara daukaka ABU, Allah Ya kawo dawwamammen zaman lafiya a ABU Zariya, amin. Daga Amiru Isa Bakori 07068147933.
Koke ga masarautar Gusau

Salam Editan jarida mai farin jini (Aminiya) don Allah ku isar man da koke na ga masarautar Gusau da kuma rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ganin irin cin mutuncin da jami’an sashen yaki da ta’addanci wato (CTU) ke yi wa jama’a, musamman masu kananan sana’o’i kamar  ‘yan acaba da ma sauran masu ababen hawa ba tare da shaidar aikata kowane irin laifi ba da kuma garkame su, ba tare da sakin su ba har sai an biya kudin beli. Fatan babban mu Mai Martaba Sarki zai dubi wannan koke nawa. Wassalam. Daga Nasiru Bello Gusau +2347068223562 [email protected]