✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Ogun ce kan gaba a jarabawar NECO

Hukumar Jarabawa ta NECO ta fitar da sakamakon jarabawar sakendire inda jihar Ogun take kan gaba a kan sauran jihohi da kashi 91 da digo…

Hukumar Jarabawa ta NECO ta fitar da sakamakon jarabawar sakendire inda jihar Ogun take kan gaba a kan sauran jihohi da kashi 91 da digo 42 cikin dari.
 
Kididdigar da aka yi ta gano cewa Akwa Ibom ta zo ta biyu da kashi 87 da digo 97 cikin dari sai jihar Zamfara da ta zo ta karshe da kashi 12 da digo 90 cikin dari duk da cewa dalibai 230 ne kawai suka zana jarabawar daga jihar.
 
Dangane da magudin jarabawa kuwa jihar Filato ita take kan gaba da kashi 21 da digo 31 cikin dari sai jihar Oyo wacce take da kashi 19 da digo 97 cikin dari.