✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Oyo ta janye tallafin wata-wata don kwashe shara

Gwamnatin Jihar Oyo ta janye tallafin Naira miliyan 30 da take kashewa a kowane wata domin kwashe kazantar shara a kan hanyoyin jihar. Daga yanzu…

Gwamnatin Jihar Oyo ta janye tallafin Naira miliyan 30 da take kashewa a kowane wata domin kwashe kazantar shara a kan hanyoyin jihar. Daga yanzu mazauna jihar ne za su rika biyan kudade daga cikin aljihunsu ga kamfanonin kwasar shara da za su fara gudanar da wannan aiki ba tare da bata lokaci ba.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, wanda ya ce daukar wannan mataki ya zama dole saboda lurar da ya yi cewa birnin Ibadan, hedkwatar Jihar Oyo yana neman komawa matsayinsa na baya, na daya daga cikin birane mafi kazanta a Najeriya.
Gwamnan ya fadi haka ne a birnin Ibadan a lokacin da ya yi wata ganawa da wakilan ma’aikatar tsaftace muhalli da shugabannin kananan hukumomi da kuma wakilan kamfanoni kwasar shara a jihar. Ya ce: “Mun yanke shawarar canza salo da za mu rika samun kudaden shiga daga sharar kazanta da mutane suke jibgewa a kan hanyoyi. Daga yanzu ba za mu ci gaba da kashe Naira miliyan 30 a kowane wata domin yin wannan aiki ba.”
Ya ci gaba da cewa: “Dukkan ma’aikatan da suke yin wannan aiki a karkashin hukumar tsaftace muhalli ta jihar za su ci gaba da yin aikin nasu ne a karkashin kamfanoni masu zaman kansu da za su fara karbar kudaden kwasar shara daga hannun jama’a. Babu wanda za a kora daga aikinsa a dalilin wannan sabon salo, a maimakon haka ma wannan hanya ce ta samar da guraben ayyuka ga jama’a.”
Ya nemi kamfanonin kwasar shara fiye da 300 da su tabbatar da cewa sun yi aiki kamar yadda ’yan kwangilolinsu suka tsara domin tsaftace jihar daga kazanta. “Abun da muke gudanarwa a yau, ya yi daidai da manufar gwamnati da ta shafi kiwon lafiya da tsaftace biranen jihar da samar da ayyuka.”
Da yawa daga cikin mutane da ke zaune a birnin Ibadan da wakilinmu ya tattauna da su dangane da wannan al’amari sun nuna farin cikinsu ne da matakin janye tallafin da gwamnati ta yi, wanda zai tilasta jama’a biyan ladar sharar d ake fitowa daga gidajensu. Alfa Murana Akinpelu cewa ya yi: “Wannan salo da gwamnati ta fito da shi ya yi kyau domin shi ne zai sa mutanen da ke zaune a birnin Ibadan su iya tsaftace muhallinsu da sanin amfaninsa”
Shi kuwa Alhaji Bashir dan’azimi Ali cewa ya yi: “A Najeriya ne kadai ake samun mahukunta suna ware wani kaso na kudin jama’a a matsayin tallafi wanda babu irin haka a kasashen da suka ci gaba. Matakin da gwamnan ya dauka na janye tallafin kwasar shara ya yi daidai.”