✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Sakkwato ta samu nasarar tura yara makaranta

Jihar Sakkwato ta samu nasarar rage yawan yaran da ba su zuwa makaranta daga kashi 69 cikin dari a 2015 zuwa kashi 36 a bana,…

Jihar Sakkwato ta samu nasarar rage yawan yaran da ba su zuwa makaranta daga kashi 69 cikin dari a 2015 zuwa kashi 36 a bana, kamar yadda kididdigar Hukumar Kula da Yara ta Majalisar dinkin Duniya ta tabbatar.

Babban jami’in hukumar mai kula da jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara, Muhammad Muhuiddin ne ya fadi haka a wurin walimar cin abinci da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta shirya masa bayan kammala rangadinsa a jihohin.

Ya ce a kididdigar da hukumar ta gudanar, ta bayyana cewa adadin yaran da ba su zuwa makaranta ya ragu fiye da kashi 50 cikin dari.

“Zuciyata ta yi fari, ganin yadda shugabannin siyasa da ayarin gwamnati suke aiki da hukumar UNICEF a bangarori da dama da suka shafi ci gaban yara a Jihar Sakkwato. Mun cin ma bukatarmu ta samun sakamako mai kyau a kasar nan. Nakan gamsu a duk lokacin da muka kaddamar da aiki kuma alfanunsa ya bayyana ga jama’a.

“Wani abu mafi muhimmanci a wurina, shi ne ganin yawaitar yara mata a makarantun kauyuka a kullum a wani rangadin duba ayyukka da na yi. A wata firamare a karamar Hukumar Binji, na samu wani aji da yara 48, mata 36, maza ne 12. Wannan ma’auni ne mai kyau, da fatan zai dore,” a cewarsa.

Jami’in ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta kara matsa kaimi musamman ga harkar allurar rigakafin shan inna, domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu nan da shekara biyu masu zuwa.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya jinjina wa Muhuiddin kan jajircewa da kokarinsa na ganin an samu ci gaba. Ya ce al’umma a jihar za su yi kewarsa kan hobbasar da ya nuna na son jama’a da yi masu hidima.