✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Zamfara na bin Gwamnatin Tarayya bashin Naira biliyan 57

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce tana bin Gwamnatin Tarayya bashin Naira biliyan 57, wadanda ta kashe wajen gina hanyoyin tarayya da ke sassan jihar daga…

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce tana bin Gwamnatin Tarayya bashin Naira biliyan 57, wadanda ta kashe wajen gina hanyoyin tarayya da ke sassan jihar daga shekarar 2011 zuwa 2015.
Kwamishinan Ayyuka na jihar, Alhaji Mu’azu Nalado ya bayyana haka ga manema labarai a ofishinsa, inda ya kara da cewa tuni babban kwamitin ayyukan na Majalisar Wakilai ya gayyaci ma’aikatarsa don samun cikakken bayani kan yadda aka kashe kudin da jihar ke bin Gwamnatin Tarayyar don ganin yadda za ta biya wadannan kudi.
Kwamishina Nalado ya kara da cewa idan Gwamnatin Tarayya ta biya jihar wadannan kudi, za su taimaka wajen samar da karin abubuwan more rayuwa ga al’ummar jihar.
Sai Kwamishina Nalado ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gaggauta biyan wadannan kudi domin jihar ta samu sukunin warware wasu daga cikin matsalolinta tare da ciyar da jihar gaba.
Kwamishinan ya kuma ce gwamnatin jihar ta bai wa Kamfanin Mother Cat kwangilar fadada Madatsar Ruwa ta Gusau kan Naira miliyan 606 don samar da ingantatcen ruwan sha ga al’ummar Gusau da kewaye.
Sai Kwamishinan ya yi kira ga al’ummar Jihar Zamfara su ci gaba da bai wa gwamnatin jihar a karkashin jagorancin Gwamna Abdul’aziz Yari Abubakar goyon bayan da ya dace domin ta samu sukunin samar musu da abubuwan inganta rayuwa a daukacin jihar.