✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jika ya kashe kakansa a Imo

Wani matashi mai suna Chukwuebuka Umunna, mai kimanin shekara 22 da haihuwa, da ke kauyen Umuoke Otulu Ahiara, karmar Hukumar Ahiazu Mbaise Jihar   Imo, ya…

Wani matashi mai suna Chukwuebuka Umunna, mai kimanin shekara 22 da haihuwa, da ke kauyen Umuoke Otulu Ahiara, karmar Hukumar Ahiazu Mbaise Jihar   Imo, ya kashe kakansa Anusiem Umunna, mai kimanin shekaru 80 da haihuwa.
Bayanan da Aminiya ta samu sun ce kakan ne ya bukaci jikan nasa chukwuebuka ya je ya saro masa sanduna a daji da zai yi turakun doya da za ta rika bi tana yado. Bayan da ya dawo daga dajin ne sai kakan ya zaunar da shi yana yi masa nasiha, cewa ya zama mutumin kirki. Ashe wannan huduba ba ta yi masa dadi ba, harzuka shi ma ta yi.
dan uwan wanda ake zargi da kisan ya kori kanensa mai suna Chigaemezu Umunna daga gidan, ya ce ya fita ya bar gidan, bayan da aka jima ya dawo gida sai ya iske aika-aikar da yayan nasa ya yi na kashe masu kaka. “Na iske shi kwance cikin jini a kan kujerarsa, duk an sassare shi da adda, jini ta baka ta hanci yana fita. Nan take na kwarma ihu don makwabta su kawo dauki.” Inji shi.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Imo, DSP Andrew Enwerem, ya tabbatar mana da labarin, ya kara da cewa: “Wannan laifi ne na kisan kai kuma rundunarmu na nan tana gudanar da bincike, tabbas laifin da ake zargi, an aikata shi.