✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Kama Da Wane’: Fim mai koyar da darussa ga magidanta

A kwanakin baya ne Kamfanin shirya fina-finan Hausa mai suna Abnur Entertainment ya kammala daukar fim dinsa mai suna ‘Kama Da Wane’ a Kaduna.Abdul Amart…

A kwanakin baya ne Kamfanin shirya fina-finan Hausa mai suna Abnur Entertainment ya kammala daukar fim dinsa mai suna ‘Kama Da Wane’ a Kaduna.
Abdul Amart ne ya shirya fim din, Adam A Zango ya ba da labari, Yakubu M Kumo ya tsara labarin fim din, inda Mu’azzam Idi Yari ya ba da umarni.
‘Kama Da Wane’ labari ne a kan wani magidanci mai suna Yasir (Adam A Zango) da matarsa Hasiya (Jamila Nagudu). Yana da babban kamfani, inda kullum ake nuna shi cikin hada-hada, a takaice dai kullum cikin aiki yake kamar agogo, duk da wannan aikin da yake yi, idan ya koma gida da daddare sai ya samu matarsa ba ta kammala dafa abinci ba, hakan ya sa ransa ya baci, kullum cikin yi mata fada, ba tare da ya karbi uzurinta ba.
Duk da haka takan yi masa zakakan kalamai masu kwantar da hankali, don nuna masa cewa za a gyara, kuma yanayin aikin gida ya gaji haka, amma duk da haka sai ya yi kememe ya rika cewa ba komai ba ne ya jawo hakan face lalaci irin nata.
Ana cikin haka kullum sai faman fada da bambami yake yi, ba tare da ya ga canji ba, hakan ya kai shi bango, inda ya kira ta ya ce mata ya gaji da wannan halin nata na lalaci, tun da ta yi karatun boko, to za a yi canji, ta koma tafiyar da harkokin ofis, shi kuma zai lura da gida, har ya cika mata baki idan tana kammala abincin rana karfe 1 to zai kammala 12, idan tana gama abincin dare karfe 7, to zai kammala karfe 5.
Matarsa ta nuna masa hakan ba karamin ganganci ba ne, amma ya kekesa kasa ya ce dole sai an yi abin da ya ce, don ya nuna mata lalaci ne kawai ke hana ta kammala ayyukan gida da wuri. Hakan kuwa aka yi.
Abubuwa da yawa sun faru wanda ya zama darasi ga magidanta.