✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kamshin kudi ya farfado da mutumin da ya shafe shekara 1 a sume 1

Wani mutum mai tsananin son kudi, wanda ya shafe fiye da shekara a sume, da nas din asibiti ta kada kudi a gaban hancinsa sai…

Wani mutum mai tsananin son kudi, wanda ya shafe fiye da shekara a sume, da nas din asibiti ta kada kudi a gaban hancinsa sai ya farfado. An yi hakan ne don a tuna masa abin da ya saba da shi.

diao Li, dan shekara 30 ya some ne a cikin Agustan 2013, bayan ya shafe fiye da mako guda bai yi barci ba, inda ya tare a shagon kwamfuta yana bincike kan dabarun kasuwanci a shafukan intanet.
Nasa-nas da ke aiki a asibitin Shenzen da ke kasar Sin, sun yanke shawarar kada masa takardun kudi a gaban karan hancinsa, a kokarin da suka yi na jawo hankalinsa ya farfado, saboda ’yan uwansa sun bayyana musu yadda yake da matukar son kudi.
Wani abin mamaki, sai kawai aka ga ya fara farfadowa daga dogon barcin da ya yi.
Shugaban asibitin, Dokta Liu Tang. Ya ce: “Mun tambayi iyayensa mene ne yake maukar kauna, sai suka ce babu abin da yake tsananin so irin kudi.”
“Da muka samu labarin tssananin soyayyarsa da kudi, sai muka yi gwaji da takardun kudi. Mun samu daurin kudin Yuan ’yan 100-100, sababbi, sai muka kanga su a gaban hancinsa, al’amarin da ya yi matukar tasiri.
Dokta Tang ya ce sun ga diao ya yi yunkurin kwace kudin, wadanda kimarsu ta kai Fam na Ingila 10, lokacin da yake ta kyafta ido.
“Al’amarin na da matukar ban mamaki, ban taba ganin irin wannan al’amari ba, tsawon shekara 20 da na yi ina aikin likita. Wannan ya nuna tunanin kamshin da kara na da matukar tasiri wajen zaburar da mutum,” inji shi.
Yanzu ’yan uwan diao sun tare a gefen gadonsa, suna amfani da wannan dabarar a asibitin Shenzen, inda yake ta farfadowa a hankali, a hankali.
Dokta Liu ya ce: “Har yanzu akwai sauran aikin kafin a sallame shi daga asibiti, amma dai yana samun murmurewa da kwarai da gaske.”