✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kani ya kashe yayansa saboda kayan sawa a Kano

Wannan magana da ya yi masa ta fusata shi don haka kawai ya lalubo almakashi ya burma masa a kirji.

A ranar Lahadi ne mazauna unguwar Kurna Babban Layi da ke Karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano suka shiga cikin firgici bayan samun labarin wani matashi da ake zargi da kisan yayansa.

Tunda farko Aminiya ta samu labarin cewa matashin mai suna Khalifa Hamza ya yi amfani da almakashi wajen kisan yayan nasa mai suna Usman Hamza saboda ya nuna bacin rai kan ya sanya masa kaya a jikinsa.

A yanzu haka dai tuni wanda ake zargi da kisan ya cika wandonsa da iska inda aka neme shi sama ko kasa aka rasa.

Sai dai ba kamar yadda aka yi ta yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa rigimar ta faru ne akan kyanwa kamar yadda mahaifin yaran ya bayyana.

Alhaji Hamza shi ne mahaifin matasan ya bayyana wa Aminiya cewa “Marigayin ya dawo gida bayan ya ya gayyato abokansa buda baki a nan gidanmu.

“Sai ya ga kaninsa ya sanya masa rigarsa da wando, don haka ya yi masa magana cewa me ya sa ya daukar masa kaya yana sawa, har yana gaya masa cewa ai mahaifiyarsu ta hana shi daukar masa kaya.

“Wai ashe wannan magana da ya yi masa ta fusata shi don haka kawai ya lalubo almakashi a aljihunsa ya soka wa yayan nasa a kirjinsa.’’

Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yi alkawarin gudanar da bincike kafin bayar da cikakken bayani a kai.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, bai ce komai ba.