✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kansila ya auri mata biyu a lokaci guda

A dai dai lokacin da ‘yan Najeriya ke shirin zaman dirshen a gida da kuma yin nesa-nesa da juna domin biyayya ga matakan kariyar cutar…

A dai dai lokacin da ‘yan Najeriya ke shirin zaman dirshen a gida da kuma yin nesa-nesa da juna domin biyayya ga matakan kariyar cutar Coronavirus, shi kuwa wani kansila a Jihar Nasarawa ya angwance ne da amarensa biyu a lokaci guda.

Kansilan mai suna Ibrahim Oboshi da ke wakiltar mazabar Iwogu a yankin Keana ya angwance ne inda aka daura masa aure da amaransa biyu wato Nazira Ozegya da Rabi Akose, an kuma jere sunayensu uku, da angon da amaransa a cikin katin gayyatar daurin aure guda.

An daura auren Kansilan da amaryarsa ta farko Nazira da misalin karfe 10 a yankin Keana yayin da aka daura aure na biyu da amaryarsa Rabi da misalin karfe 12 duk a ranar 28 ga watan Maris inda aka shirya wa su ukun gagarumin bukin da kek guda daya.

Duka da kasancewarsa zababben kansila, Ibrahim Oboshi na alfahari ne da kasancewarsa manomi.