✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

karamar hukuma za ta kashe Naira biliyan 2.3 a Jigawa

karamar Hukumar Taura da ke Jihar Jigawa za ta mayar da hankali wajen ayyukan raya kasa a wannan shekara tare kuma da samar da kayan…

karamar Hukumar Taura da ke Jihar Jigawa za ta mayar da hankali wajen ayyukan raya kasa a wannan shekara tare kuma da samar da kayan jin dadi ga al’ummar yankin. Shugaban karamar Hukumar ta Taura, Malam Abdulmajid Isma’ila Chakwai-kwaiwa ne ya sanar da manema labarai haka, jim kadan bayan ganawa da zauran majalisar jihar, inda ya kare kasafin kudin da karamar hukumar za ta kashe a bana.

Ya kara da cewar karamar hukumar za ta mayar da hankali ne wajen bunkasa harkokin aikin gona da raya ilimi da samar wa matasa aikin yi da inganta harkokin lafiya da ruwan sha a yankunan karkara da nufin inganta rayuwar jama’a.

Ya ce gwamnatinsa za ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta taimaka wa matasa sun dogara da kansu ta hanyar horar da su sana’ar hannu domin su tsaya da kafarsu. Ya ce majalisar jihar ta amince musu su kashe Naira biliyan biyu da miliyan 300 a bana. “bangaren ilimi da ayyukan kananan hukumomi su ne za su fi cin kaso mafi girma daga cikin abin da karamar hukumar ta ware domin kashewa a  bana, sannan sai bangaren ilimi yake mara musu baya”  inji Shugaban.