✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karuwa ta fallasa mai buga jabun kudi

Dubun wani da ake zargin cewa ya kware wajen buga jabun kudi ta cika a yayin da ’yan sanda a Jihar Kaduna suka kama shi…

Dubun wani da ake zargin cewa ya kware wajen buga jabun kudi ta cika a yayin da ’yan sanda a Jihar Kaduna suka kama shi bayan da wata karuwa ta gano kudin da aka ba ta na jabu ne.
Rundunar ta gabatar da wanda ake zargin tare da abokan sana’ar sa ga manema labarai a sakatariyarta da ke Kaduna.
Wanda ake zargin mai suna Dabid Kwabe, mazaunin garin Abuja ne kuma an ce ya kware wajen buga jabun takardun kudi kafin dubunsa ta cika.
Dabid Kwabe ya ce bai ji dadi ba da aka ce masa wai karuwa ce a Zariya ta gano kudin da aka ba ta na jabune har hakan ya sa aka kama shi.
Ya ce ya kammala karatunsa ne a fannin Harkar Kasuwanci, kuma yana da shagon buga takardu a Abuja tare da sayar da injunan buga takardu. Kuma an kama shi ne a lokacin da ya je bayar da wani inji ga wani abokin cinikinsa.
Sai dai a cewar ’yan sanda sai da aka kama wani mai suna Sani Abubakar wanda shi ke yawon kashe jabun kudin a Zariya, shi kuma ya taimaka aka kama Kwabe. “A ranar 30 ga Yuli, 2014, da misalin karfe 8:00 na dare wani mai suna Sani Abubakar dan shekara 23, kuma mazaunin kofar Jatau, Zariya ya ziyarci wata karuwa a dakinta inda ya biya ta Naira 1,500 bayan ya biya bukatarsa ita kuma sai ta lura kudin jabu ne ya ba ta, nan take ta nemi jama’a su kai mata dauki aka kama shi daga nan sai aka kira ’yan sanda,” inji majiyar.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Umar Shehu ya ce bayan an yi wa matashin tambayoyi ne sai ya tabbatar da aikata laifin ya kuma ce shi ma wani ne mai suna Sabo Umar ya ba shi kudin.
Ya ce bayan ’yan sanda sun kama Sabo shi kuma sai ya ambaci Dabid Kwabe mai shekara 37 da ke gida mai lamba Flat A Block 6 of Gaduwa Estate, Abuja inda kuma aka same shi da injinan buga jabun kudin.
Kwamishinan ya ce: “Da aka gudanar da bincike a gidajensu mun gano Naira dubu 60 na jabu ’yan Naira dari biyar-biyar sai kuma kwamfuta da suke amfani da ita. Dukkansu sun amince da aikata laifin don haka nan ba da dadewa ba za mu tura su kotu.”