✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karuwai da masu gidajen giya na cin karensu babu babbaka a Dange-Shuni

Al’ummar Unguwar Rumbukawa Remon billage da ke cikin karamar Hukumar Dange Shuni sun sun koka kan yadda masu sayar da giya da karuwai suke cin…

Al’ummar Unguwar Rumbukawa Remon billage da ke cikin karamar Hukumar Dange Shuni sun sun koka kan yadda masu sayar da giya da karuwai suke cin karensu babu babbak sakamakon daurin gindin da suke samu daga mahukuntan yankin duk da yin hakan ya saba wa yarjejeniyar da suka yi da su na ba za su yi duk wani aikin barna a shiyyar ba saboda wurin na Musulmi ne kuma Hausawa.
daya daga cikin mutanen unguwar da ya zanta da Aminiya kuma ya nemi a sakaya sunansa ya ce “A wannan unguwa tamu  Hausawa ne tsantsa, kabilun Ibo suka nemi a sayar musu filaye don su zauna a wurin, mun amince amma sai da aka yi yarjejeniya da su cewa ba za a yi gidan mata masu zaman kansu ba wato karuwai, sannan ba za a sayar da giya ko tabar wiwi da duk wani aikin barna ba kuma suka yarda tun da farko.  Haka muka fara zama da su, da tafiya ta yi nisa sai suka fara canjawa har abin ya yi kamari muka sanar da hukuma a wancan lokaci aka zo aka watsa wurin don ya zama matattarar barayi.”
 Majiyar ta ci gaba da cewa “Bayan dogon lokaci suka dawo yanzu abin assha da suke yi har ya fi na farko sai muka sake daukar mataki muka kai takardar koke ga jami’an tsaro gaba daya na jihar nan da Ardon Shuni, saboda  unguwar na  karkashin kulawarsa amma har yanzu da nake magana da kai kasuwancinsu sai kara ci gaba yake yi, tarbiyyar ’ya’yanmu na kara sukurkucewa saboda ba wani mataki da aka dauka.
Ya ce “Mun zargin manyan yankin ne da laifin daure wa mutanen gindi ne saboda a kwanan nan ne aka yi rigima tsakanin masu sayar da giya da wata mata mai sayar da ruwan leda a wurin kan sai ta bayar da kudin kungiya Naira  dubu goma saboda duk wanda zai yi sana’a a wurin sai ya bayar da su in ko ta ki bayar da kudin za su tashe ta daga wurin don su ne ke da wurin a yanzu saboda sun riga sun zauna da wani basarake ya ba su goyon baya da umarnin su rika rufewa daga karfe 11 zuwa 12 na dare. Kan wannan duk mutanen unguwarmu suna fadin shi ne ya ba su damar su ci gaba da sayar da giyarsu, shi ne kuma ya hana kokarinmu ya yi nasara duk da wurin barna ne da gwamnati ke fada shi,’ inji shi.
Hafsat Sani wata da ta yi zama a daya daga cikin dakunan unguwar amma yanzu ta bar wurin, ta shaida wa wakilinmu cewa: “Na bar wurin ne saboda an sace min dana a wasu kwanaki da suka gabata, inda ina kwance misalin karfe uku na dare kawai wani mutum da ake kira Tijjani sarauyin wata da muke  gida day tare ya tayar da ni ina barci ya fada min wai ya ji kukan mota wani ya fado gidan sun tafi da dana. Ni na dauka wasa ne amma ya tabbatar min da gaskiyarsa inda ya sanar da ’yan sanda suka zo gidan, suka same ni, ina kuka na fada musu Tijjani ne ya dauke min da don na taba kama shi ya dauke shi a cikin wani dare kuma a lokacin da ya tayar da ni, kofar gida a rufe take kuma ban ji kukan mota ba, a hakan dai aka tura mu Hedikwatar ’Yan sandan Jihar  kan wannan, bayan kwana biyar aka bayar da shi beli ta hanyar budurwarsa a kan Naira dubu 250, kamar yadda na ji tana fadi da bakinta ta yi belin kanta. Daga nan na bar gidan da unguwar gaba daya don gudun sake faruwar wani abu kuma har yanzu da nake magana da kai ban ga yarona ba duk da akwai yara da yawa a gidan amma ba a sace su ba sai nawa.  Na yi bakin ciki kan wannan abin da ya faru da ni. Ina kira ga masu ruwa-da-tsaki  su tayar da mutanen da ke wurin don matattara ce ta miyagun mutane.”  A garin Kwannawa a karamar Hukumar Dange Shunin cikin unguwar Shaf-Kwana an samu gawar wata mace a cikin dakinta da ake kira Patience a ranar Lahadin da ta gabata, inda ake zargin an yi mata yankan rago kuma tana kwance cikin jini. Ana zargin wani da ya zo wurinta ne ya yi lalata da ita, ya yanka ta sannan ya tafi da wayarta ta kimanin Naira dubu 40. Kuma a daren ’yan sanda suka tafi da maigidan da duk wadanda ke cikin gidan domin bincike.
Kan abubuwan da ake zargi suna faruwa a yankin, wakilinmu ya nemi jin ta bakin Shugaban karamar Hukumar, Alhaji Mode dan Tasalla, inda ya ce: “Ban yi wata daya da shiga ofis ba, kuma ban kai ga takardarsu ba, in na kai za mu dauki mataki a gwamnatance,” daga nan ya kashe waya.
Da Aminiya ta je fadar Ardon Shuni, Alhaji Muhammad Jabbi sai aka ce ta dakata Ardon yana tare da baki, daga baya sai Sakataren Masarautar ya nemi ya zo ofishinsa domin yi masa bayanin dalilin zuwansa.   Bayan ya yi masa bayani ne sai Sakataren ya aika wani don ya sanar da Ardon, amma sai Ardon ya bugo masa waya cewa a fada wa wakilin Aminiya ba zai samar damar ganinsa ba saboda ba ya jin dadi.
Aminiya ta zanta Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Almustafa Sani ya tabbatar masa da kisan matar da aka yi a Shaf-Kwana kuma ya ce suna kan bincike, kuma za su dauki matakin da ya dace ga wadannan batagarin da suka addabi mutanen Remon billage nan ba da dadewa ba.