✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karyewar gada ta jawo faduwar shugaban majalisar Gombe a zabe

Al’ummar yankin Yamaltu ta Yamma da suka hada garuruwan Wade da difa da Lubo da Kinafa a karamar Hukumar Yamaltu-Deba a Jihar Gombe sun botsare…

Al’ummar yankin Yamaltu ta Yamma da suka hada garuruwan Wade da difa da Lubo da Kinafa a karamar Hukumar Yamaltu-Deba a Jihar Gombe sun botsare wa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Alhaji Inuwa Garba a zaben makon jiya, inda suka ki zabensa ya sake komawa majalisar a karo na hudu saboda rashin yin katabus, musamman kan gadarsu da ta karye.

Alhaji Inuwa Garba, ya fadi a zaben ne bisa zargin cewa jama’arsa ba su amfana da komai ba a jagorancin
da ya yi musu na tsawon shekara goma sha biyu a matsayin wakili daga yankin Yamaltu ta Yamma.
Gadar Moron da ke Zambuk wacce ta hade garuruwan ta karye sakamakon ambaliyar ruwa a bara, kuma gadar ce ta hade garin Shugaban Majalisar da sauran garuruwan yankin.
Aminiya ta ziyarci garin a lokacin da ake gudanar da zaben gwamnoni da ’yan majalisar jihohi inda ta zanta da wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaye sunansa, inda ya ce faduwar wakilin nasu wato Shugaban Majalisar na da alaka ne da rashin gyara musu wannan gada da ta karye a shekarar 2013.
“A lokacin damina idan aka yi ruwa ba mu da wata hanya sai ta gefen gadar, muddin muna son mu wuce sai mun jira ruwa ya dauke inda mukan yi sa’o’i biyu zuwa uku muna jira,” inji majiyar.
Wakilinmu ya zanta da zababben dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Yamaltu a Jam’iyyar APC, Ustaz Yunusa Abubakar, inda ya ce an jima da gina gadar tun yana dan majalisar jihar a shekarar 2003, lokacin Sanata danjuma Goje yana Gwamna amma da ta karye sai gwamnatin dankwambo ta ki gyara ta.
Ustaz Yunusa Abubakar, ya ce maimakon tunda dansu yana Shugaban Majalisar Jihar ko a kasafin kudin a sa ya kuma matsa wa Gwamna a gyara ta sai bai yi hakan ba.
Ya ce a lokacin damina ba sa iya bin hanyar sai sun yi zagaye ta Daben Fulani ta Malam Sidi a karamar Hukumar Kwami sannan su fita. “Gadar ta hade garuruwan hakimai bakwai da suka hada da Gwanin Yamma da Lubo mahaifar Shugaban Majalisar, sai difa da Daben Fulani da Jurara da Malleri.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Alhaji Inuwa Garba a garinsu na Lubo lokacin da manema labarai suka same shi a ranar zaben amma sai ya daga musu hannu ya ce ba zai gansu ba yana ganawa da mutane.