✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘kasa da dutse’

Assalamu alaikum, Manyan Gobe, yaya sanyi? Da fatan ana nazarin karatu a yanzu da ake hutu. A yau na kawo muku wani labari ne da…

Assalamu alaikum, Manyan Gobe, yaya sanyi? Da fatan ana nazarin karatu a yanzu da ake hutu. A yau na kawo muku wani labari ne da na yi masa take da: ‘kasa da dutse.’ Labarin na kunshe da yadda rubutu a kasa bai cika yin tasiri ba kamar rubutun da aka yi a kan dutse.  Asha karatu lafiya.

Bala da Sule aminan juna ne. Ran nan suka tafi daji domin neman itace sai musu ya kaure a tsakaninsu, nan take Bala ya  kwashe Sule da mari.
Abin sai ya bata wa Sule rai amma sai ya ki ya rama. Sai ya rubuta a kasa cewa “Yau aminina ya mare ni.” Hakan da yayi ya sa Bala ya ji kunya.
Suna cikin tafiya sai suka ga rafi. Suka tsaya domin su yi wanka kafin su nemo itacen. Can sai Sule ya fara nitso a ruwa. Ganin hakan, Bala sai ya sauri ya taimaka wa Sule. Sai ya samu kusa ya rubuta a kan dutse cewa “Yau aminina Bala ya ceci rayuwata.”
Ganin hakan, sai Bala ya ce “Da na mare ka, ka rubuta a kasa cewa na mare ka amma yanzu kuma ka yi rubutu a kan dutse cewa na cece ka, ko me ya sa ka yi haka?”
Sai Sule ya ce idan an bata mana rai ya kamata mu zama masu hakuri. Shi ya sa na yi rubutu a kasa domin rubutu a kan kasa ba shi da tasiri kuma iska za ta iya gogewa. Amma da ka taimaka min, na yi rubutu ne a kan dutse don kada ya yi saurin gogewa domin ba kyau mutum ya yi saurin mantawa da alherin da aka yi masa. Don haka rubutu a kan dutse ba zai yi saurin gogewa ba kamar rubutu a kasa.
Da fatan Manyan Gobe za su koyi juriya da hakuri a duk lokacin da ransu ya baci.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi