✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasafin kudi: Gwamnatin Tarayya za ta karbo bashin Dala biliyan 2

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta karbo bashin Dala biliyan 2 daga Bankin Duniya da kuma Bankin Bunkasa Afirka (AfDB) don cike gibin da za…

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta karbo bashin Dala biliyan 2 daga Bankin Duniya da kuma Bankin Bunkasa Afirka (AfDB) don cike gibin da za a samu a kasafin kudin bana.

Tun a shekarun baya ne Najeriya ta kulla yarjejeniyar karbar bashi daga wadannan bankuna, inda aka rada wa yarjejeniyar suna ‘Shirin Karbar Bashi ta 2012-2015’.
Makadusin wannan bashin shi ne, don magance harkokin da suka shafi cinikayya da kasashen waje da kuma dawo da darajar Naira.
Ministar kudi da kuma tafiyar da tattalin arziki, Dokta Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana dalilan da za su sanya a ciwo bashin a lokacin da take tattaunawa da ’yan jarida a Abuja kan matakan farfado da darajar Naira da cinikayya da kasashen waje da kuma kasafin kudin 2015.
“Mun dade da fara tattaunawa da wadansu bankuna wadanda suka hada da Bankin Duniya da kuma Bankin Bunkasa Afirka, dama akwai kudaden da suka ajiye mana sakamakon yarjejeniyar karbar bashi da muka cimma da su. A yanzu mun bukaci za mu karbi wadannan kudade don cike gibin da za a samu a kasafin kudi. Mun bukaci Dala biliyan 2 daga wurinsu.” Inji ta.
Ministar ta bukaci ’yan Najeriya su rika daukar matakan da za su bunkasa asusun ajiyar waje na Najeriya, wadanda za su farfado da darajar Naira.
Ta kuma bayyana a cikin mutane dubu 66 da suka nemi shiga tsarin karbar bashi don mallakar gidaje a karkashin Hukumar Bada Lamuni ta Najeriya mutane dubu 40 sun samu nasarar cika dukkan ka’idoji da sharuddan da aka sanya, inda har mutane dari 300 suka kai ga mallakar gidaje.
Ta jaddada duk da faduwar farashin man fetur nan gaba tattalin arzikin kasar nan zai bunkasa.