✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasashen Larabawa sun bukaci sojojin Isra’ila su fice daga Gaza

Kungiyar Kasashen Larabawa ta bukaci Isra'ila da ta takatar da kisan gillar da take wa Falasdinawa a yankin Zirin Gaza.

Kungiyar Kasashen Larabawa ta bukaci Isra’ila da ta takatar da kisan gillar da take wa Falasdinawa a yankin Zirin Gaza.

Sakatare-Janar na kungiyar, Ahmed Aboul Gheit, ya kuma yi tir da hare-haren na Isra’ila, wanda ya a matsayin tsantsar “tauye hakkin Falasdinawa” ne a matsayinsu da ’yan Adam.

Ya bayyana a taron kungiyar a birnin Baghdad na kasar Iraki cewa, “Muna kira ga Isra’ila ta gaggauta janye sojojinta ta bude hanyoyin kai wa Falasdinawa agaji.”

Ahmed Aboul Gheit ya ce yanke ruwan sha da wutar lantarki da man fetur da hanyoyin sufurin abinci zuwa Gaza ba komai ba ne face yunkurin yi wa Falasdinawa kisan kare dangi.

Isra’ila ta kashe Falasdinwa sama da 2,700 cikin mako guda a Zirin Gaza, inda jiragenta suke luguden bama-bamai, sojoji suke kai samame ta kasa.

Isra’ila, wadda ta shafe shekaru tana kwace yankunan Falasdinawa tare da kame su tana tsarewa kan zargin kai mata hari, ta bayyana luguden bama-baman da take a Gaza a matsayin matakin kawar da kungiyar Hamas da ke kawo mata harin ta’addanci daga yankin.