✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Kashe $1.5bn wajen gyara matatar man Fatakwal almubazzaranci ne’

Hamshakin dan kasuwar ya bayyana yunkurin a matsayin wani mataki na barnar kudade na ba gaira ba dalili.

Wani fitaccen dan kasuwa kuma mamallakin bankin Stanbic IBTC a Najeriya, Mista Atedo Peterside ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da yunkurin da take yi na kashe kimanin Dalar Amurka biliyan daya da rabi wajen gyara matatar mai ta Fatakwal.

Hamshakin dan kasuwar, a cikin wani sako da ya wallafa a sahfinsa na Twitter ranar Litinin ya bayyana yunkurin a matsayin wani mataki na barnar kudade na ba gaira ba dalili.

Ya ce, “Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dakatar da yunkurin da take yi na kashe $1.5bn wurin gyara matatar man Fatakwal saboda barnar kudi ce tsagwaronta kuma lamarin na janyo cece-kuce a kasa.”

Mista Peterside wanda kuma shine shugaban Gidauniyar Anap ya kuma ce kamata ya yi gwamnatin a maimakon hakan ta yi nazari kan shawarar da kwararru suka ba ta ta duba yuwuwar sayar da matatar ga ’yan kasuwa.

“Kwararru da dama sun bayar da shawarar cewa abin da zai fi amfani shine a sayar da wannan matatar domin a ba masu zuba jari damar tafiyar da ita har ta dawo aiki ka’in da na’in da kudadensu.”

Ko a makon da ya gabata dai sai da tsohon Mataimakin Shaugaban Kasa Atiku Abubakar ya kalubalanci yunkurin na gwamnati wanda ya ce kamata ya yi ma a bincike shi.

Ya kuma ba da shawarar cewa kamata ya yi sayar da ita sannan a yi amfani da kudaden wajen samarwa da mutane ayyukan yi.