✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwancin kifi akwai riba – Hadiza Musa

Kasuwancin kifi akwai riba – Hadiza Musa Aminiya: Yaya sunanki? Hadiza: Sunana Hadiza Musa: Ni ‘yar Maiduguri ce kuma nayi a kalla shekaru biyar ina…

Kasuwancin kifi akwai riba – Hadiza Musa

Aminiya: Yaya sunanki?

Hadiza: Sunana Hadiza Musa: Ni ‘yar Maiduguri ce kuma nayi a kalla shekaru biyar ina harkar kifi.

Aminiya: Kamar nawa ya kamata mutum ya fara da shi idan zai yi wannan harkar?

Hadiza: Yana da kyau mutum ya fara da dubu goma zuwa ashirin zuwa dai-dai karfin da mutum yake da shi. 

Aminiya: Kamar kifin nawa kike saya a rana?

Hadiza: Ina sayan kifin a kalla Naira dubu 150 a rana sannan na sayar.

Aminiya: Nasarori da na samu.

Hadiza: Idan mutum yana sana’a zuciyarsa daya, zai ga mai kyau. Wannan sana’ar akwai samu sannan akwai biyan bukata. Kadan daga cikin nasarorin da na samu akwai kekuna biyu da na saya, wadanda nake bayar wa haya, na sayi fili na gina gida, sannan ina biyan kudin makarantar ’ya’yana a ciki.

Babban abin farin ciki kuma shi ne, Allah Ya ba ni sa’a na taimaka wa matasa da ba su daaikin yi da aikin wankewa, inda duk wanda ya sayi kifi sannan a biya su hakkinsu. A cikin matasan da na taimakawa, akwai wadanda suka daina shaye-shaye sannan kuma akwai wadanda su ka yi aure.

Ba matasa maza kadai na taimakawa ba. Ina kuma taimaka wa matasa mata ko kuma wadanda suke da karamin karfi domin samun rufin asiri. Babu abin da zan iya cewa sai hamdala.

Aminiya: kalubale dake cikin wannan harkar?

Hadiza: A gaskiya ba a cika samun kalubale ba, sai dai ta harkar kostamomi (abokan ciniki). Wadansu sai su karbi bashi sannan ba za su biya ka ba akan lokaci. Wannan yana jawo koma baya a harkar. Domin a lokacin da kake bukatar karbar kudi ka sayi kifi sai a samu akasi. Sannan nakan fuskanci kalubalen samo wadansu nau’ukan kifi, kamar su kurungu da karfasa da kuma makamantansu a wasu kauyuka ko rafi. Wata rana har kananan hukumomin jiha muke zuwa domin nemo wadannan kifaye.

 Aminiya: Shawara ga wadanda ke sha’awar shiga wannan harkar?

Hadiza: Wannan sana’ar akwai samu sosai, akwai albarka. Idan ka riketa hannu biyu, za ka ga alherinta.  Ba a samun kudi a dare daya sai an yi hakuri. Da hakuri da juriya da kuma iya mu’amala da mutane wannan shi ne babban abin da ke kawo cigaba da nasara a wannan harkar. Domin na yi a kalla shekaru goma sha biyar wajen sayar da kifi, kuma har ila yau ina yi.

Shawara ga matasa masu zaman banza

Zaman banza ba shi da amfani. Yana da kyau matasa su tashi su yi wa kansu. Babu sana’a da take kadan. Kowace irin sana’a ce. Akwai matasa da ke karkashina wadanda a sakamakon wannan harkar sun yi aure sannan wadansu sun bar shaye-shaye, wasu suna makaranta a ciki wasu kuma suna ciyar da iyayensu a ciki. Duk kaskancin sana’a tafi zaman banza.