✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kaurace wa kayan Faransa ya kamata Musulmi su yi ba zanga-zanga ba – Sheikh Sa’idu Jingir

Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya ce kaurace wa kayayyakin Faransa ya…

Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya ce kaurace wa kayayyakin Faransa ya kamata Musulmi su yi ba zanga-zanga kan zanen batanci da mujallar Charlie Hebdo ta yi ga Manzon Allah ba.

Sheikh Sa’idu Jingir ya ce zanen batanci wata masifa ce mara iyaka da babu wanda zai ce ga iyakarta. Ya ce “Ba zanga-zanga ya kamata mu Musulmi mu yi ba idan irin wannan al’amari ya faru. Zanga-zanga wani al’amari ne da ke nuna cewa kamar ka yarda an fi karfinka ke nan. Abin da ya kamata mu yi shi ne kasashen Musulmi su yanke huldar jakadanci da Faransa, kuma mu kaurace wa kayayyakin kasar.”
Ya ce kada a yi zanga-zanga kada a zagi kowa ko kona kayansa, a kaurace wa kayan Faransa a daina karanta jaridunsu da sauraron gidajen rediyonsu, sai ranar da suka ce abin da mujallar ta yi bai dace ba, don haka za su hukunta su, sannan a dawo hulda da su.