✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kimiyya ce ginshikin ci gaban duniya – UNESCO

Kimiyya ce ginshikin ci gaban duniya - UNESCO

Shugabar Hukumar Bunkasa Ilimi da Al’adu ta Duniya (UNESCO), Audrey Azoulay, ta ce kimiyya na da matukar tasiri wajen tabbatar da ci gaban duniya.

Ta bayyana haka ne a cikin wani sakon da ta gabatar na albarkacin bikin ranar kimiyya ta duniya don haɓaka zaman lafiya da ci gaba.

A cewarta, kimiyya ce ta taimaka wajen rage yaɗuwar cututtuka kamar annobar COVID-19, baƙon dauro da foliyo ta hanyar samar da allurar rigakafi.

Haka kuma, ta ce UNESCO na tunawa da ranar Kimiyya ta Duniya ce don inganta zaman lafiya da ci gaba a kowace shekara tare da jaddada muhimmancin da kimiyya take da shi.

A bana dai, bikin ya zo daidai da lokacin bikin shekarar ilimi ta ƙasa da ƙasa don samar da ci gaba mai ɗorewa, wadda daga bisani za ta shiga cikin shekaru 10 na kimiyyar ƙasa da ƙasa don ci gaba mai dorewa daga 2024 zuwa 2033.

Bugu da ƙari ari, Azoulay ta bayyana jajircewar UNESCO wajen tallafa wa bincike na kimiyya, wanda aka misalta ta hanyar shawarwarinta na 2021 a kan haɓaka kimiyya.

“UNESCO tana aiki domin haɓaka daidaiton jinsi a fagen kimiyya, gami da shirye-shirye a nahiyar Afirka da yankin Caribbean tare da haɗin gwiwar gidauniyar L’Oréal.

“A cikin shekarun da suka gabata, wannan hadin gwiwa ya karfafa ayyukan masana kimiyya mata fiye da 4,100 da suka fito daga kasashe sama da 110,” in ji ta.

Wannan shi ne babban taron ranar Kimiyya ta Duniya kuma na bana zai gudana ne a hedikwatar UNESCO a ranar 13 ga Nuwamban 2023.

Manufar wannan taron shi ne a karfafa dogaro ga kimiyya ta hanyar magance kalubalen da suka jiɓanci ilimin kimiyya, sada kimiyya daidai da bukatun al’umma da kuma ba da kariya da tabbatar da ’yancin masana kimiyya.