✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kiristoci 50 sun ci gajiyar auren Tata

Kiristoci 50 na daga cikin mutum 600 da suka ci gajiyar auren da Alhaji Abdullahi Umar Tsauri ya dauki nauyin gudanarwa a ranakun Juma’a da…

Kiristoci 50 na daga cikin mutum 600 da suka ci gajiyar auren da Alhaji Abdullahi Umar Tsauri ya dauki nauyin gudanarwa a ranakun Juma’a da Asabar da suka gabata.
An gudanar da bikin daurin aure ne a Masallacin Juma’a na Izala da ke kan titin Zariya da kuma cocin Grace Baptism dukansu a garin Funtuwa da ke Jihar Katsina.
 Da yake jawabi wanda ya dauki nauyin auren ta hanyar biya wa angwayen sadakin Naira dubu 20 kowannensu tare da yi wa amare kayan lefe, da na daki dab gara da kuma ba su jarin gudanar da sana’a, Alhaji Umar Abdullahi Tsauri wanda aka fi sani da Tata ya ce, yana bayar da wannan gudunmawa ga marayu da gajiyayyu ne saboda ganin yadda iyaye suke neman taimakon aurar da ’ya’yansu maza ko mata.
Alhaji Tata ya ce, cikin ka’idoji da sharuddan da ’yan kwamiti ke la’akari da su akwai tabbatar da cewa ba a dauki kason wata karamar hukuma an kai wata ba. Kuma ma’auratan su zamo suna da ilimin addini gwargwado, ango kuma ya zamo yana da sana’a.
Wasu daga cikin jagororin Kiristocin da aka aurar, wato Barau da Ibrahim Sani sun bayyana wa manema labarai cewa wannan shiri na aure da Tata yake yi, wani tsari ne da zai kara hada kan jama’ar Jihar Katsina da kasa baki daya. “A saninmu kuma a tarihi ba mu taba jin an ce ga wani mutun daya ba gwamnati ba yana yin haka, hasali muna da bambancin addini amma ya shigo cikinmu ya nemi marayunmu da mabukatanmu ba tare da nuna bambanci ba ya aurar da ’ya’yanmu mutum 100 wato maza 50 mata 50 kuma bisa tsarin addininmu kuma a wajen ibadarmu. Kuma duk kayan da iyaye suke yi wa ’ya’yansu, Tata ya yi wa ’ya’yanmu bai bambanta ba, kuma bai kawo mana wani sharadi ba.”
Ibrahim ya ce, ba kowa ne ke irin aiki ba sai mutumin Allah, a kan haka ya ce, kamata ya yi jama’a su rika yi masa kyakkyawar fata. “Koda aiko Tata aka yi kamar yadda wasu ke cewa, to ya isar da sako,” inji Ibrahim.
Shi ma Malam Muhammadu daya daga cikin wadanda aka aurar da ’ya’yansu ya ce, babu abin da za su ce wa wannan mutum sai addu’a.
kananan hukumomi 11 da ke shiyyar ta Funtuwa da aka tsamo wadannan marayu da marasa galihu aka aurar sun hada da: Matazu 25, Musawa 25, kankara 40, Faskari 40, kafur 60, danja 27, Sabuwa 26, dandume 31, Malumfashi 100, Bakori 70, Funtuwa 106, sai Kiristoci 50.