✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kiwon kaji: Yadda aka yi wa masu neman tallafi damfarar N819m a Kano

An yi wa masu kiwon kaji a Kano damfarar Naira miliyan 819 da sunan shirin tallafin Gwamnatin Tarayya.

An yi wa masu kiwon kaji a Jihar Kano damfarar Naira miliyan 819 a karkashin wani shirin tallafin bogi da sunan Gwamnatin Tarayya.

Masu kiwon kajin su 4,500, sun zargi Kungiyar Adashin Gata Domin Noman Zamani na Najeriya (NAMCON) da damfara da cuta da kuma zaluntar su, a karkashin shirin tallafa wa masu kiwon kaji.

Wakilin masu kiwon kajin, Alhaji Nafi’u Isyaku Danbatta, ya ce “A 2021/2022 NAMCON ta gabatar mana wani kyakkyawan shirin tallafin noma ta bukaci kowannenmu ya biya N182,000 a matsayin kudin rajista.

“Abin da suka karba daga hannunmu Naira miliyan 189, amma daga karshe suka ki cika alkawarin da suka yi mana”

Alhaji Nafi’u ya ci gaba da cewa, NAMCON ta yi wa kowane mai kiwon kaji a cikinsu alkawarin ba shi ’yan tsaki guda 1,000 ’yan kwana daya da haihuwa tare da abincinsu da kuma kayan aikin kiwo.

Sannan ta yi alkawarin bai wa kowannensu fuloti mai fadin 50X50 tare da ba su horo na tsawon kwana hudu, amma da lokacin ya zo, sai ta ki yin duk abin da ta yi alkawarin.

Ya bayyana haka ne a taron da Hukumar Karbar Korafin Al’umma ta Kasa ta shirya a Jihar Kano domin sauraron jama’a, da niyyar binciken ayyukan kungiyoyin adashin gata marasa rajista a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Alhaji Nafi’u ya ce zambar da NAMCON ta yi wa mambobinsu a Jihar Kano ta jefa su cikin halin ha’ula’i.

A jawabinsa, Daraktan Hukumar na Kasa a Jihar Kano, Ahmed Ado Dadinkowa, ya ce za su binciki lamarin da duk sauran zarge-zargen da aka gabatar domin tabbatar da hukunta masu laifi.

Shi ma Daraktan Binciken Kamfanoni na Hukumar, Barista Ewa Udu, ya bukaci hukumomin da ke kula da harkokin kungiyoyin adashin gata da su tashi haikan domin hana faruwar irin haka.