✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Koriya ta Arewa kasar ta’addanci ce – Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya fara shirye-shiryen kakaba wa kasar Koriya ta Arewa wasu sabbin takunkumi bayan sanar da cewa kasar tana goyon bayan ta’addanci.…

Shugaban Amurka Donald Trump ya fara shirye-shiryen kakaba wa kasar Koriya ta Arewa wasu sabbin takunkumi bayan sanar da cewa kasar tana goyon bayan ta’addanci.

Bayan wannan sanarwa ta shugaba Trump, yanzu Koriya ta Arewa ta shiga sahun Iran da Sudan da Syria a matsain kasashen ta’addanci, wanda ke nuni da cewa za a kakaba wa kasar wasu takunkumi bisa shirinsu na makamashin nukiliya.

Tuni Shugaba Trump ya sanar da cewa Sashen Al’amuran Dukiyar za ta sanya wa Koriya ta Arewa takunkumi, a shirin Trump na dakile hanyoyin samun kudin kasar, domin hana ta ci gaba da shirinta na Nukiliya kamar yadda Yahoo ta ruwaito.

“Wannan ne zai zama takunkumi mafi tsauri da za a kakaba wa kasar,” inji Trump.

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka, Red Tillerson ya ce dama kasar tana cikin wasu takunkumi da dama, domin har ta fara shiga cikin mawuyacn hali a yanzu. Tillerson ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa kasar na fama da karancin man fetur, domin ana samun dogon layi a tashohin man fetur da iskan gas, kuma kudin shigar kasar ya yi kasa.

Tun a watan Satumba, Trump ya umarci kasar Amurka ta ladabtar da duk kamfanin da yake hulda da Koriya ta Arewa, inda ya bada umarni ga sashen kula da al’amuran kudede da ta bincika duk wani kamfani da ke harkallar kayayyaki ko kimiyyar zamani da kasar Koriya ta Arewa, kuma ta hana kamfanin hulda a Amurka.

Haka kuma Tillerson ya bukaci kasar China, wadda ita ce ke da kashi 90 a cikin kasashen da ke hulda da Koriya ta Arewa da ta dakatar da harkallar mai da kasar.

Tillerson ya ce yadda Koriya ta Arewa ta dan dakata da shirin na wata biyu abu ne mai kyau, sannan ya ce za a iya yin sulhu idan suka nemi sulhun, inda ya ce idan aka kakaba wa kasar takunkumi mai tsauri, shugaba Kim zai saurara, “Wannan ne kadai hanyar da za ayi maganinka har sai ka zo teburin sulhu.”

Ayyana kasar a matsayin kasar ta’addanci zai kara tayar da kura tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa, wanda suka dade suna sa zare. Amma sai dai Koriya ta Arewa ba ta nuna alamar jan baya a shirinta na makamashin na nukiliya.