✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kudin shiga: Najeriya za ta samu raguwar kashi 25 a 2015

Kasancewar man Najeriya ta dogara da man fetur wajen samun kashi 94 cikin 100 na kudin shiga, inda a yanzu kuma farashin man fetur ya…

Kasancewar man Najeriya ta dogara da man fetur wajen samun kashi 94 cikin 100 na kudin shiga, inda a yanzu kuma farashin man fetur ya yi mummunar faduwa a kasuwanni duniya, hakan ya sanya aka yi hasashen Gwamnatin Tarayya za ta samu raguwar kashi 21 zuwa 25 cikin 100 na kudin shigar da za ta samu a shekarar 2015. 

Manajin Daraktan Hukumar tattara bayanai kan kudin shiga, Mista Bismarck Rewane ya yi wannan hasashen a lokacin da yake jawabi cikin wata takarda da ya gabatar mai suna ‘Declining Rebenues: Time for new ideas a lokacin taron da kamfanin Remita ya shirya a Legas a ranar Lahadi.
A yayin taron wanda aka shirya shi kan yadda za a samo sabbin hanyoyin samar da kudin shiga, Mista Rewane ya bayyana kudin ayyukan EIU ya karu daga Dala biliyan 10.5 zuwa Dala biliyan 27.5 a cikin wannan shekara (2015), wanda hakan yake alakanta za a samu raguwar kashi 75 cikin 100 na asusun ajiyar gwamnatin tarayya.
Rewane ya yi shakkar cewa ba lallai ba ne raguwar farashin wadansu kayayyaki ya taimaka wa gibin kudin shigar da ake samu daga man fetur don daidaituwar cinikayya har tattalin arziki ya ci gaba da bunkasa.
Ya tabbatar da cewa yin amfani da hanyoyin sadarwa (ICT) na daya daga cikin hanyar da za a kara samun kudin shiga.
“ICT hanya ce ta kara samun kudin shiga da kuma saukaka wa masu biyan kudin haraji.” Inji shi.
Ya ce za a iya amfani da ICT wajen samun kudin shiga idan aka samar da muhallin yin amfani da ICT ba tare da tsada ba, ko aka kwadaita wa masu biyan kudin haraji romon da za su samu a ICT, sannan a bijiro da hanyoyin horar da mutane don su kware a fannoninsu da kuma ta hanyar tallace-tallace don shirin ya samu karbuwa.
Ya ce Allah Ya wadata Najeriya da kamfanonin sadarwa kamarsu SystemSpec da za su iya kirkiro hanyoyin da za su taimaka wajen samun kudi shiga.