✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kujerar dan majalisa: Ban gamsu da nasarar NNPP ba, zan tafi kotu – Dan Ganduje

Tuni dai ya tafi kotu don neman bin ba'asi

Umar Abdullahi Ganduje, dan Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, wanda ya tsaya takarar dan Majalisar Wakilai a jam’iyyar APC, ya ce bai yarda da sakamakon zaben da ya ba NNPP nasara ba.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai ta ayyana Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe a matsayin wanda ya lashe kujerar dan majalisar a mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado, a jam’iyyar NNPP.

Tuni dai Umar, wanda aka fi sani da Abba Ganduje ya maka Tijjani Jobe a gaban kotun sauraron kararrakin zabe.

Abba, ta bakin lauyansa, Barista A.T Falola, ya kuma kalubalanci INEC kan ayyana Jobe a matsayin dan takarar da ya samu rinjayen kuri’un da aka kada a lokacin zaben.

Da ya ke gabatar da kara a gaban kotun, Falola ya roki kotun da ta gudanar da shari’ar a kan Jobe da kuma jam’iyarsa ta NNPP mai sakatariya a unguwar Sharada a Kano