✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar addini a Kano ta yi tir da Amurka dangane da kudus

Kungiyar Jama’atu Tajdid Islamiy (JTI) reshen Jihar Kano ta gudanar da taron lacca don nuna rashin amincewa ga matakin da kasar Amurka ta dauka na…

Kungiyar Jama’atu Tajdid Islamiy (JTI) reshen Jihar Kano ta gudanar da taron lacca don nuna rashin amincewa ga matakin da kasar Amurka ta dauka na ayyana birnin Jerusalam a matsyain hedikwatar kasar Isra’ila.

A jawabinsa, Shugaban kungiyar reshen Jihar Kano, Malam Abdullahi Saluhu Aikawa ya bayyana cewa hakki ne a kan dukkanin Musulmin duniya su yi kokarin kare Masallacin kudus, kamar yadda za su kare masallatai masu alfarma na Makka da Madina.

“Wajibi ne dukkanin Musulmi mu fahimci cewa masallacin kudus shi ne masallaci na uku bayan masallacin Harami da na Manzon Allah (saw) da ya wajaba a kan Musulmi ya kare shi daga dukkanin wata cutarwa. Don haka muke Allah wadai da wannan mataki da Amurka ta dauka.”

Tun da farko Malamin sai da ya tabo tarihin rigingimun Falasdinawa, wanda ya ce ya samo asali ne tun kafin shekarar 1948. Ya yi kira ga Musulmi da kada su ja da baya wajen ci gaba da nuna rashin amincewa a kan wannan lamari har zuwa lokacin da Amurkaza ta janye wannan kuduri nata.

A nasa jawabin, Ustaz Yahaya Tanko ya bayyana cewa wannan lamari ya shafi dukkanin Musulmin duniya, idan aka yi la’akari da koyarwar addinin Musulnuci game da ’yan uwantaka. “Addinin Musulunci ya hore mu Musulmi da mu hada kai don haka abin da ya shafi Musulmin da ke Faladinu ya shafi duk Musulmin duniya, don haka mu ma a nan muke taya ’yan uwanmu Falasdinawa wadanda ke cikin wani hali don yin tirjiya ga matakin na Amurka.”

Jama’a da dama ne suka halarci taron wanda ya hada da Shugaban Majalisar kolin Malaman Jihar Kano, Shaikh Ibrahim Khalil da Malam Aliyu Ali Abubakar Babban Sakataren kungiyar JIBWIS da Dokta Muhammad Babangida na BUK da Malam Nafi’u Salisu Zangon Barebari da Malam Nuru Adam da Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa na BUK da sauransu.