✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalejin Ilimi ta Izala ta rantsar da sababbin dalibai 189 a Gombe

An rantsar da sababbin dalibai 189 na shekarar karatu ta 2018/2019 na Kwalejin Ilimi na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS  College of…

An rantsar da sababbin dalibai 189 na shekarar karatu ta 2018/2019 na Kwalejin Ilimi na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS  College of Education) da ke Gombe.

Kwalejin wanda marigayi Sheikh Isma’ila Idris Jos ya kafa, tana ba da horo ne a bangaren ilimin addini da zamani, inda take bayar da takardar shaidar malanta ta kasa (NEC) kan ilimi da sauran kwasa-kwasai goma.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kwalejin Malam Muhammad Dan’azumi, kira ya yi ga sababbin daliban su kaurace wa dabi’un da ba su dace ba irin shan miyagun kwayoyi da shiga kungiyar asiri da kuma sanya tufafin da ba su dace ba.

Hakimin Kurba, Alhaji Abubakar Habu Kurba, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwalejin kira ya yi ga Kungiyar Izala ta ninka kokarinta wajen kara samar da wasu makarantu da kayayyakin kyutata rayuwa da za su taimaka wajen kara inganta ilimin matasa don ba su damar yin gogayya da ’yan uwansu da suka kammala karatu a wasu manyan cibiyoyin ilimi a fadin kasar nan.

Da yake jawabin godiya, Farfesa Mahmood Baba daga Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, taya sababbin daliban murnar samun shiga kwalejin ya yi inda ya hore su da su yi karatu sosai don kada su yi wasa da damar da suka samu.

Farfesa Mahmmod Baba, ya sake yin kira ga daliban cewa su guje wa munanan dabi’u da suke lalata dabi’un daliban manyan jami’oin kasar nan, sannan su zama jakadun kwalejin nagari.

A tsokacin Shugaban Majalisar Zartarwar Kwalejin, Sheikh Hamza Adamu Abdulhamid, cewa ya yi kwalejin na bukatar tallafi musamman a bangaren kayayyakin aiki don bai wa kwalejin damar kara daukar wasu dalibai masu yawa a nan gaba.