✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwallon Kwando: Kobe Bryant ya yi murabus

Shahararren dan kwallon Kwando na Amurka na kungiyar LA Lakers, Kobe Bryant ya yi murabus bayan ya kwashe shekaru ashirin yana bajinta. A wasansa na…

Shahararren dan kwallon Kwando na Amurka na kungiyar LA Lakers, Kobe Bryant ya yi murabus bayan ya kwashe shekaru ashirin yana bajinta. A wasansa na karshe ya ci kwallaye 60 a kan kungiyar kwallon Kwando ta Utah Jazz inda aka tashi 101-96.
 Ya fara wasan kwarraru ne yana da shekaru 17 a shekarar 1996. Ya zama dan wasa mafi shahara watau MbP a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2008. Sannan dan wasan ne ya jagoranci kungiyarsa wajen lashe kofuna a gasar kwallon kwando a shekarun 2000 da 2001 da 2002 da 2009 da kuma a 2010.  Sannan yana cikin wadanda suka lashe wa Amurka lambobin zinare a gasar Olamfik da ta gudana a shekarar 2008 da kuma 2012.
 An sayar da tikitin wasansa na karshe ne a kan Dala dubu 27 da500 wanda ya yi daidai da Naira dubu 800  maimakon Dala dubu 1 ko Dala dubu 2 da aka saba sayarwa.
 Kobe Braynt a jawabinsa na ban kwana ya ce: “Na gode wa jama’a da abokaina da takwarorina da iyalaina kan goyon bayan da suka ba ni”.
 Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kwando ta Najeriya Mista Scambo Morrison ya ce “Ya yaba masa matuka don ya cimma burinsa a wasan kwallon kwando.  Sannan ya yaba da murabus din da ya yi don ya ba na baya dama su ma su nuna tasu bajintar a wasan kwallon kwando.