✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamishina Baraka ta koma PDP

Tsohuwar Kwanishinar Gona ta Jihar Kano, Dokta Baraka Sani wacce ta ajiye mukaminta a makon jiya ta koma Jam’iyyar PDP.Aminiya ta gano cewa tuni tsohuwar…

Tsohuwar Kwanishinar Gona ta Jihar Kano, Dokta Baraka Sani wacce ta ajiye mukaminta a makon jiya ta koma Jam’iyyar PDP.
Aminiya ta gano cewa tuni tsohuwar Kwamishinar ta hade da tsofaffin ’yan jam’iyyarta ta PDP a kramar Hukumar Nassarawa inda ta fito.
Yayin da aka tuntube ta a waya Dokta Baraka Sani ta tabbatar da komawarta Jam’iyyar PDP, jam’iyyar da ta bari lokacin da Gwamna Rabi’u Kwankwao ya koma Jam’iyyar APC a watannin baya.
Dokta Baraka Sani ta bayyana wa Aminiya cewa ta sauka daga mukaminta ta kuma bar Jam’iyyar APC ne saboda rigingimun siyasa a mazabarta. “Gaskiya ne na bar Jamiyyar APC, kuma na koma tsohuwar jam’iyyata ta PDP. Na gode,” inji ta lokacin da take amsa tambayoyin wakilanmu.
Wakilan Aminiya sun ji cewa Kwamishinar ta koma PDP ne sakamakon rigingimun da suka dabaibaye batun zaben kananan hukumomomi mai zuwa da za a yi a jihar a ranar 17 ga watan Mayu.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa an samu rashin jituwa a tsakanin Dokta Baraka da Gwamna Kwankwaso a lokacin da ta kai sunan dan takararta, inda Gwamnan ya sa kafa ya shure tare da bayar da sunan wani daban, lamarin da aka ce bai yi mata dadi ba.
Yayin da aka tuntubi Shugaban Rikon na Jam’iyyar APC a Jihar Kano Injinya Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce ba zai yi magana akan batun ba sai Gwamnan Jihar ya dawo daga tafiyar da ya yi kasar waje.