✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.  Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya…

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.  Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya sanya yin kyauta da kyauta-yi cikin kyawawan dabi’un Musulmi.  Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma ya koyar da cewa kyauta da kyauta-yi ba ta rage dukiya; Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.  
Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu, (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.
Bayan haka, yau, kamar yadda kanun mukala ya nuna, za mu duba dabi’ar kyauta da kyauta-yi ne, kamar yadda bayanin haka ya zo a cikin littafin Shakhsiyyatul Muslim Kama Yasughuhal Islam Fiy Alkitab Wassunnah na Dokta Muhammad Ali al-Hashimi, tare da wasu bayanai daban. Allah Ya ba mu dacewa wajen bi da kuma aiwatar da wannan dabi’a, wadda ba ta sa talauci, don mu samu rabauta duniyarmu da lahirarmu.
Malam ya ce: Babu shakka duk Musulmi na gaskiya, wanda yake da yakinin bin karantarwar addininsa, zai kasance mai kyauta ne shi, mai kyauta-yi ta yadda zai ta bibiyar hanyoyin da zai ga ya kyautata wa al’ummar da ke kewaye da shi, a kowane yanayi da lokaci, wato yana cikin wadata ne ko rashi.
A duk lokacin da wannan Musulmi ya yi kyauta don Allah, to yakan bayar ne da dadin zuciya, alhali yana sane da cewa ba asara ya yi ba, kuma ba barna ya yi ba, domin yana sane da cewa Allah, Wanda Yake sane da komai, Ya tanada masa abin a wajenSa. Allah Ta’ala Ya ce, “…. Kuma duk abin da kuka ciyar daga alheri, to lallai Allah, gare shi (abin da kuka ciyar din), Masani ne.” Surar Bakarah, aya ta 273.
Haka nan ya yi imanin cewa duk abin da ya kashe a cikin kyauta-yi (saboda Allah), abin zai komo gare shi, kuma za a nunnunka masa shi, Allah Ya ribanya masa lada, a nan duniya da kuma Lahira, kamar yadda Allah Ya ce, “Misalin wadanda suke ciyar da dukiyoyinsu don yada kalmar Allah, kamar misalin kwaya daya ce, sai ta fitar da zangarniya guda bakwai, kowace zangarniya kuma a cikinta (aka samu) kwaya dari. Kuma Allah Yana ninkawa ga wanda Ya ga dama, kuma Allah, Mai yalwa (yalwata wa kowa) ne, Masani ne.” Surar Bakarah, aya ta 261.
A cikin littafin Tarjama da Sharhin Ma’anonin Alkur’ani Mai Girma, a shafi na 230, Shaikh Ja’afar Mahmud Adam ya ce, “Abin nufi, misalin wadanda suke ciyar da dukiyoyinsu don yada kalmar Allah, don taimakon addinin Musulunci, …kamar misalin kwaya daya ce…da aka shuka ta a cikin kasa…sai ta fitar da zangarniya guda bakwai, kowace zangarniya kuma a cikinta… aka samu kwaya dari, ka ga za a ninka wa mutum har sau dari bakwai ke nan.  Ubangiji Ta’ala Ya ce, “…Yana ninkawa ga wanda Ya ga dama…” gwargwadon kyakkyawar niyyar mutum lokacin da zai ciyar da dukiya din, kuma Shi (Allah), Mai yalwa ne, kuma Masani ne.
“Hadisi ya tabbata a cikin Sahihi Muslim [na1151], Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya nuna yadda Allah Yake ninninka wa mutum aiki nagari. Kowane aiki, kyakkyawan aiki daya, za a iya ninninka wa mutum sau goma; ba ma sau goma ba, za a ninka wa mutum har sau dari bakwai. Wani Hadisi ya sake tabbata a cikin Sahihi Muslim (na 1892),  Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), zai tafi wani jihadi, sai wani Balarabe ya kawo taimakon taguwa guda daya tare da akalarta a daure da ita. Da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya karba, sai ya ce, “A ranar tashin Alkiyama Ubangiji Ta’ala Zai maye maka gurbi,  sakamakon wannan guda daya da taguwa guda dari bakwai kowace da akalarta.” Abin nufi, wannan kinaya ce zuwa ga lada da za a ninninka wa mutum a ranar tashin kiyama.”
Allah Yana sane kuma Yana musanyawa: Allah Ya ce, “….Kuma abin da kuka ciyar daga wani abu, to, Shi (Allah) ne Zai musanya shi…” Surar Saba’i, aya ta 39.
Haka nan Allah Ya ce, “….Kuma duk abin da kuka ciyar na alheri, to domin kawunanku ne, kuma ba fa za ku ciyar ba, sai don neman yardar Allah, kuma duk abin da kuka ciyar na alheri, za a cika muku (ladarsa), alhali da dai, ba za a zalunce ku ba.” Surar Bakarah, aya ta 272.
Musulmi na gaskiya yana bayar da dukiyarsa ne alhali yana da yakinin Allah Zai maye masa gurbinta ta fuskar sanya wa abin da ta baro (sauran) albarka, ga kuma ninki na lada a wajenSa. Kuma idan ya makale ta (dukiyar), ya yi rowa, ya ki bayarwa (saboda tsoron talauci), to sai Allah Ya tauye ta, Ya saka masa asara, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya fadi cewa, “Duk safiya, idan bayin Allah suka tashi, sai wasu Mala’iku biyu su sauko. daya yana addu’a cewa, “Ya Allah, Ka musanya wa wanda ya yi kyauta da dukiyarsa;” dayan kuma yana cewa, “Ya Allah, Ka sanya asara ga mai rowa.”  Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
A wani Hadisin kudusi, Allah Yana cewa, “Ciyar (bayar; yi kyauta) da dukiyarka, ya kai dan Adam, Ni kuma in ciyar da kai (in ba ka, in yi maka kyautar) dukiya.” Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
Musulmin da ya yarda da Allah, ba ya wata shakka a cikin zuciyarsa, in ya bayar (ya yi kyauta) saboda Allah, cewa dukiyarsa ta ragu don ya yi haka, sai ma dai karuwa take yi, kamar yadda Hadisin da Muslim ya ruwaito ya nuna, cewa, Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Sadaka (kyauta ko ciyarwa saboda Allah, ko fitar da zakka ta farilla, misali) ba ta rage dukiya….”
Ladar da ake samu a dukiyar da aka kyautar saboda Allah tana da yawa domin Allah Yana nunnunkata ninkin-ba-ninkin, kamar yadda bayani ya gabata).  Shi ya sa ma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), yakan ce, “Dukiyar da take taskance ita ce wadda aka bayar da ita saboda Allah.” A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ba da labarin wata tunkiya da aka yanka, aka yi ta rabon namanta, har sai lokacin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya tambayi ko me ya rage a cikinta, sai aka ce masa, “Karfata daya.” Sai ya ce, “An taskance komai na tunkiya, sai karfata daya kadai.” Imamu Tirmiziy ne ya ruwaito shi kuma ya ce Hadisi ne mai kyau, ingantacce.
Wato manufa, an taskance ladar kowane sashi na tunkiyar ban da karfata daya, wadda suka ci.  Shi ya sa Bahaushe ma kan ce, “Abin da ka bayar, shi ne naka, abin da ka ci kuwa na salga (masai) ne.”
Allah Ya ba mu dacewa da abin da yake alheri.
Nan za mu dakata, sai makon gobe, in Allah Ya kai mu.
Wassalamu alaikum warahmatullah!