✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

La-Liga:  An sanya ranar da Barcelona da Madrid za su kara

A ranar Talatar da ta gabata ce Hukumar Kwallon Kafa ta Spain ta bayyana sabuwar ranar da kungiyar kwallon kafa na FC Barcelona da takwararta…

A ranar Talatar da ta gabata ce Hukumar Kwallon Kafa ta Spain ta bayyana sabuwar ranar da kungiyar kwallon kafa na FC Barcelona da takwararta Real Madrid za su gwabza.

Wasan da ake yi wa lakabi da El-Clasico zai gudana ne a ranar Laraba 18 ga Disamba mai zuwa maimakon gobe Asabar 26 ga wannan wata da muke ciki.

Hukumar ta canja ranar yin wasan daga gobe ne saboda yamutsin da ke faruwa a tsakanin masu zanga-zanga da  ’yan sanda a yankin Kataloniya, inda kulob din Barcelona yake da zama.

Jim kadan bayan wata kotu a Spain ta yanke hukuncin daurin shekara 9 zuwa 13 ga wadansu shugabannin Kalatoniya da aka same su da laifin neman ballewa daga kasar Spain ne magoya bayansu suka shiga yin fito-na-fito da jami’an tsaro al’amarin da ya tilasta dage wasan El-Clasico zuwa wata rana ta daban.

Wasan El-Clasico shi ne wasa mafi zafi a Gasar La-Liga inda aka kiyasta kimanin mutum miliyan 500 ne suke kallon wasan a sassan duniya.