✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarin abokai biyu

Akwai wasu abokai guda biyu sun nufi shiga gari sun taso daga kauye. Suna cikin wasanni da hira a yayin da suke tafiya. Sai dayan…

Akwai wasu abokai guda biyu sun nufi shiga gari sun taso daga kauye. Suna cikin wasanni da hira a yayin da suke tafiya. Sai dayan ya ce Allah ya sa idan suka shiga birni su yi nasara. dayan ya ce amin.

Da suka nufi wani bishiya kusa da wani rafi sai suka ga wani abu a bakar leda. Sai dayan ya ce kada su taba wannan ledar. dayan ya ce shi sai ya ga mene ne a ciki.
Sai ya samu sanda ya bude ledar da ita. Sai ya ga kudi masu dinbin yawa. Nan take ya ce “Alhamdulillah yau kam na yi nasara domin na yi kudi”. Sai dayan abokin ya ce da shi kada ka ce “ka yi kudi, kace mun yi kudi domin ai tare muka tsinta”.
dayan ya ki sam ya kuma ce ba zai bai wa dayan ko sisi ba.
Ashe barayi ne suka ajiye kudin a wajen. Abokan na cikin tafiya sai suka yi hadu da ‘yan sanda. Suka ce wannan kudin waye ? Sai wanda aka yi wa rowa ya ce na abokinsa ne. Sai aka kama abokin mai rowa ,dayan kuma ya wuce birni.