✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ladan N50,000 za a bani na kai dauri 173 na tabar wiwi Daura’

Kudin basu zo hannuna ba tukunna har sai na isar da wannan sako.

Wani dan shekara 50 mai suna Sunday Isaac, ya shiga hannu Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) da dauri 173 na tabar wiwi a kan hanyarsa ta zuwa garin Daura daga Zariya.

Aminiya ta samu cewa an yi wa mutumin alkawarin biyanshi Naira dubu hamsin a matsayin ladan kai wannan kayan maye Jihar Katsina.

Da yake zanta wa da manema labarai bayan holensa da jami’an tsaro suka gudanar, mutumin ya ce kudin basu zo hannunsa ba tukunna har sai ya isar da wannan sako.

Bayanai sun ce Isaac ya shiga hannu ne tare da wani karen mota mai suna Hamisu Salisu, sai dai direban motar da ya dauko dakon kayan ya tsere.

Kakakin NSCDC a Jihar Katsina, DSC Muhammad Tukur wanda ya inganta rahoton, ya ce tuni sun mika ababen zargin a hannun Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyin ta Kasa (NDLEA).

A cewarsa, “mun samu nasarar kama shi ne bayan samun bayanan sirri kuma muka shiga aiki cikin hanzari, inda a karshe muka cimmai da kayan mayen da misalin karfe 7.30 na yammacin 6 ga watan Yulin 2021.

“An dauko dakon kayan ne tun daga Jihar Legas a cikin wata babbar motar daukan kaya makare da kifi na wani dillalin kifi a Jihar Katsina.”