✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Laifi ne yin amfani da kayan gwamnati don yin kamfe – Sarkin Mota

Babban direban marigayi Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Alhaji Ali Kwarbai da aka fi sani da Ali Sarkin Mota ya ce laifi ne…

Babban direban marigayi Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Alhaji Ali Kwarbai da aka fi sani da Ali Sarkin Mota ya ce laifi ne babba ga kowane mutum komai girman mukaminsa, koda Shugaban kasa ne, ya debi kudin jama’a don yin kamfe ko wata hidima ta kashin-kansa. Alhaji Ali Sarkin Mota ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Kaduna, inda ya ce, “Ya kamata a yi koyi da shugabannin Jamhuriyya ta Farko wadada burin gina kasa ne kawai a gabansu ba son kai irin na shugabannin yanzu ba, tun daga karanan hukumomi da ke da dimbin kudi da motoci a harkarsu ta ofis da gida da tulin ma’aikata da ababen da suka karya doka, amma ba mai iya yi musu magana cewa sun karya doka da yin facaka da kudin al’umma.” Dattijon ya ce marigayi Sardauna yana da motocinsa na kashin kai da yake amfani da su don yin kamfe ko wata bukata tasa ta daban. “Shi ma Firayin Ministan Najeriya Alhaji Abubakar Tafawa balewa yana da motarsa ta kansa da ke a ajiye a Kaduna don dauko matarsa ko iyalinsa daga filin jirgin saman Kaduna a kai su Bauchi ko a dawo da su, amma ba na gwamnati ba,” inji shi. Sarkin Mota ya ce “Ba za a kawar da cin hanci da rashawa ba har sai masu mulki sun rika bin doka da oda, ya ce galibin masu mulki, kafin su samu mulki mutum bai da ko kwabo, amma da zarar ya hau mulki sai ya fara bushasha da facaka kudin jama’a.”
Ya ce dan kudin da ake ba ’yan fensho ya yi kadan, shi ya sa ake samun karin almundahana da rub-da-ciki da kudin al’umma.