✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

… Leeds United ta fara zawarcin Gnabry dan kwallon Arsenal

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Leeds United da ke Ingila ya fara tuntubar kulob din Arsenal akan yiwuwar sayar masu da…

Serge Gnabry dan kwallon ArsenalA ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Leeds United da ke Ingila ya fara tuntubar kulob din Arsenal akan yiwuwar sayar masu da dan kwallon gabansu mai suna Serge Gnabry a matsayin aro kamar yadda manajan kulob din Leeds Brain McDermott ya sanar a kafar sardarwar kulob din.
Shi dai McMermott ya bayyana kudurin kulob din na cefano zaratan matasan ’yan kwallo ne a lokacin da yake hira da ’yan jaridu kafin wasan da kulob dinsa ya yi da na Bournemouthy a ranar Talatar da ta wuce, inda ya ce Gnabry na daya daga  cikin ’yan kwallon da yake nema ruwa a jallo.
Sai dai ya zuwa wannan lokaci kocin ya ce bai samu bayani daga kulob din Arsenal a kan yiwuwar sayar masa da dan kwallon ba ko akasin haka amma  har yanzu bai cire rai a kansa ba.
Shi dai Serge Ganbry, dan asalin Jamus yanzu haka tauraruwarsa tana haskakawa a kulob din Arsenal a kakar wasa ta bana musamman ganin yadda kulob din ya sanya shi gaba wajen sanya shi a wasanni a kan kari tun bayan da dan kwallon gabansu Theo Walcott ya samu rauni.