✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikacin lafiya na boge ne ya fi daga min hankali – Namashaya Diggi

Shugaban karamar Hukumar Kalgo a Jihar Kebbi,. Umar Namashaya Diggi ya bayyana cewa babban abin da ya fi daga ma sa hankali a sha’anin badakalar…

Shugaban karamar Hukumar Kalgo a Jihar Kebbi,. Umar Namashaya Diggi ya bayyana cewa babban abin da ya fi daga ma sa hankali a sha’anin badakalar ma’aikatan boge a karamar Hukumar Mulki ta Kalgo shi ne yadda ake samun malamin lafiya da ke duba marasa lafiya da takardar karya.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambaoyoyin wakilinmu a ofishinsa dake Kalgo, jim kadan bayan wata hatsaniya da wasu da ba a san ko su waye ba suka haddasa, har ma aka yi kone-konen tayu a wasu sassa na karamar hukumar a makon da ya gabata.

Namashaya Diggi ya ce ba komai ya haddasa wancan hatsaniya ba illa akan batun binciken da ya dauko ne game da masu karya da takardun boge suna karbar albashi, alhali su na da matasa wadanda suka kammala karatunsu, amma ba su samu guraban aiki ba, saboda yadda ake samun wasu ‘yan tsiraru da suka maida wannan karamar hukumar ta kalgo tamkar dakunansu, inda ya ce akwai wanda yake amsar kudi da sunan ya yi digiri alhali karya ne! akwai masu NCE na karya da ire-irensu birjik, har ma’aikatan lafiya akwai masu takardun karya. Amma ya ce abin takaici, sai ka iske mai digiri na gaskiya ana ba shi dubu 5, amma sai ka iske wanda ko furamare mai je ba, ba shi nan ba shi can, ana ba shi dubu 20 ko 18, amma ga mai digiri ga hannu dubu biyar.

“Haka kuma zaka iske wani yana amsar albashin fiye da mutum 20 shi kadai, wani ma ya sanya ‘ya’yansa da matansa duka suna karbar albashi. To da muka zo, sai muka ce wannan barnar ba za mu bari aci gaba da ita ba. Domin dama ko yaushe mai Girma Gwamna, Sanata Atiku Baguda yana ba mu shawarar cewa mu yi gaskiya, mu yi adalci kasancewar mun karbi rantsuwa da Alkur’ani cewa zamu yi adalci ga kowa, domin shi mutum ne mai son a kwatanta gaskiya koyaushe. Haka nan shi ma Mai Martaba Sarkin Gwamdu ya zagaya wurarenmu ya kara bamu shawarwari, yana cewa mu yi abin da al’umma za su amfana da damar da Allah Ya ba mu. Don haka muka dauko wannan aiki na tantance ma’aikata” a cewarsa.

Shugaban karamar hukumar ya ci gaba da cewa, “To Alhamdulillahi a lokacin da na zo na iske wannan kwamacala sai na fidda wani tsari na ‘data form’ wanda dukkan ma’aikaci zai cike dukkan bayanai game da shi. To wannan ya taimaka matuka game da tantancewar, domin mun gano abubuwa da yawan gaske, wani ko kunya babu ya cike sunayen ‘ya’yansa masu shekaru 8 da 12 da 14 duk suna karbar albashi. Wasu suna furamare wasu suna sakandare, amma duk an sanya sunayensu cikin masu karbar albashi.”

“Abubuwan dai sai dai mu ce Allah Ya sawwaka. Sannan akwai wasu dake ganin cewa idan aka bar wannan aikin ya samu nasara, masu hakkin gaskiya zasu amfana, to shi ne bai yi masu dadi ba. Sun mance Musulmai muke, kura’ani aka aza mana, kuma Allah Zai tambayemu yadda muka yi mulki ranar Alkiyama, amma suka ga ba haka ya kamata ayi ba, a bari a cigaba da bin son rai, a cigaba da danne sauran al’umma. Mu kuma muka kowa yana da hakki a wannan karamar hukuma, kuma in Allah Ya so zamu kwatanta adalci gwargwadon iko. To wannan ne fa dalilin da yasa marasa gaskiya suka shirya bore a fakaice har aka yi wadancan kone-kone,” in ji Diggi.

“To wannan fa shi ne halin da ake ciki. Kuma ba zamu fasa ba, duk wanda yake karbar albashi ba bisa ka’ida ba, zamu cire sunansa ko wanene. Wannan yaudara da suke yi da sunan ma’aikata na zanga-zanga akan albashi babu inda za ta kai su, domin ma’aikata suna da kungiya (union), kuma su ake kwatarwa hakkinsu, to me zai sa su yi bore?”

A karshe ya bayyana wakilinmu ayyukan tantancewar suna samun nasara, kuma a yanzu haka sun cimma kashi 80 cikin 100. Sannan sai ya yi kira ga dukkan al’ummar karamar Hukumar Kalgo su kara ba shi hadin kai don ciyar da yankin gaba. 

Kuma kowa ya ji tsoron Allah cikin abinda zai iya don samun nasararmu baki daya.