✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan gwamnati da sarautun gargajiya

A makon jiya ne Shugaban Ma’aikata na Tarayya Alhaji Bukar Goni Aji ya ba da sanarwar haramta wa ma’aikacin gwamnati karbar sarautar gargajiya. Hanin a…

A makon jiya ne Shugaban Ma’aikata na Tarayya Alhaji Bukar Goni Aji ya ba da sanarwar haramta wa ma’aikacin gwamnati karbar sarautar gargajiya. Hanin a cewar Goni Aji wanda ya hada da wasu ‘nau’o’in lambobin yabo,’ wani bangare ne na matakan sake fasalin aikin gwamnati. Da wannan hani ma’aikatan gwamnati za su iya karbar irin wadancan sarautu ne bayan sun bar aiki.
Takardar hanin ta yi nuni da cewa gwamnati ta fahimci cewa wasu ma’aikatan gwamnati na kamun kafa a ba su wadancan sarautu da lambobin yabo. Kuma wannan ba shi ne karo na farko ba, sai dai kuma Goni Aji ya nuna rashin jin dadin gwamnati kan halayen wasu ma’aikata wadanda a karshe hakan yana iya tado da batun gaskiya da amana. A can baya kafin takardar umarnin gwamnati ta fito, ya gargadi ma’aikatan kan su tsaya bisa ka’idojin da doka ta tanada, wadanda suka hana ma’aikatan gwamnatin gudanar da wasu ayyuka na kashin kansu. A cikin sabin gargadin Shugaban Ma’aikatan ya yi gargadin cewa keta wannan doka za a dauki shi a matsayin rashin da’a a karkashin dokokin aikin gwamnati kuma za yi hukunci a kansa kamar yadda doka ta tanada.
Hanin ya tsame wasu kadan daga ciki.Takardar ta bayyana inda ma’aikacin gwamnati zai iya rike mukamin sarautar gargajiya ya zamo, “Ya ko ta gaje shi ne ko karbar wata lambar yabo,” ta hanyar neman yarjewa daga Sakataren Gwamnatin Tarayyya ta ofishin Shugaban Ma’aikata. Lura da abubuwan da suka faru a baya, kuskure ne a tsame “sarautun gado,” daga hanin, saboda an bata hakan a baya. Don haka duk ma’aikacin da ke son sarauta sai ya zabi tsakanin ci gaba da aikin gwamnati ko sarautar gargajiya ko wadancan lambobin yabo.
Watsuwar mukaman sarautun gargajiya da masarautu ke bayarwa da kuma lambobin yabo daga kamfanoni ko cibiyoyi suna matukar kawo damuwa a baya-bayan nan. A ka’ida ma’aikacin gwamnati zai gudanar da aikinsa ne cikin sirri nesa da idon mutane ko nuna isa irin ta ’yan siyasa. Mukaman sarauta da ake ba daidaikun mutane ana yi ne domin nuna godiya kan ingantacciyar gudunmawa da suka bayar a wani bangare na rayuwa, don haka kamata ya yi a bayar da su bayan mutane sun kammala wa’adin aikinsu ba kafin haka ba. Amma a yau sabanin haka ke gudana inda bayar da sarautun gargajiya ke zama wata sila ta samun aikin da ba a gudanar ba, ko a bayar da su a ranar da mutum ya samu aiki.
A shekarun baya-bayan nan, musamman sakamakon tsara manyan mukaman gwamnati da suka kai mattsayin daraktoci kamar na mukaman siyasa, sai ma’aikatan gwamnati suka rika zamowa kurkusa tare da nuna alamun irin wannan. A yanzu matsakaita da manyan ma’aikatan gwamnati sun tsunduma ga duk wani abu na nuna iko da isa a tsakanin jama’a, kamar gudanar da bukukuwan sarautun gargajiya masu tsada da kammala su da gudanar da liyafa a kasashen waje, inda Landan da Dubai suka zamo wuraren da aka fi zaba. Wannan rayuwa ce mai tsada da kasar nan ke dandan kudarta wajen gudanar da ita.
Domin haka wajibi ne gwamnati ta fadada wannan hani ya shafi dukkan sassan ma’aikatan gwamnati ciki har kwamishinoni da mashawarta da ministoci da gwamnoni da Shugaban kasa da masu rike da mukaman siyasa da ake biyansu daga aljihun gwamnati. Ya zamo za su iya karbar irin wadancan sarautu da lambobin yabo ne kawai bayan sun sauka daga mukamansu. Cibiyoyin da suke ba da irin wadannan sarautu da lambobin yabo su kuma su farfado da mutuncin wadannan sarautu da lambobin yabo ta wajen karrama wadanda gudunmawarsu kawai aka duba wajen ba su. Baya ga haka, wadannan karramawa su zamo kan wani halin kirki ne ba wanda ya fi bayar da kudi ba. Kuma a inda aka ba da wadannan sarautu ko lambobi bisa cancanta amma daga baya aka samu mutunci ya tafka ta’asa a aikin gwamnati ko na wani kamfani, sai a janye su.
Dawo da martabar aikin gwamnati ta hanyar tabbatar da bin doka da ka’idoji abin maraba ne. Kuma akwai bukatar hakan ya zamo ya dakile haba-habar ma’aikatan gwamnati da ke bin hanyoyin sace dukiyar jama’a domin su samu a rika damawa da su ta wajen samun wadannan abubuwa. Aika takardun gwamnati kan lamarin wani abu ne daban, yayin da tabbatar ana aiki da ita shi ma wani abu ne daban. An taba daukar irin wannan mataki a baya, amma aka kasa cimma nasara. Misali Gwamnatin Soja ta Olusegun Obasanjo ta haramta wa masu rike da mukaman gwamnati ciki har da ma’aikatan gwamnati su rika watsa kudi a wurin bukukuwa. Don haka a zage dantse domin aiwatar da wannan sabon umarni kuma a tilasta shi a kan dukkan masu rike da mukaman gwamnati.