✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan lafiya

A daidai lokacin da muke ta tsakuro bayanai jefi-jefi a kan wasu al’amura da suke shafar tafiyar da fannin kiwon lafiya a kasar nan, yana…

A daidai lokacin da muke ta tsakuro bayanai jefi-jefi a kan wasu al’amura da suke shafar tafiyar da fannin kiwon lafiya a kasar nan, yana da kyau a waiwayi wata ‘matsala’ ta rashin samun jituwa tsakanin ma’aikatan lafiya da aka dade ana jin surutai a kai, domin jama’a su fahimci yadda lamarin yake. Akwai ma’aikata a bangaren kiwon lafiya iri-iri wadanda idan babu su kusan harkar lafiya gurguncewa za ta yi. Misali a ce ga jirgin sama ga matuki, ai ba a ce matukin ne kawai zai iya harkar sarrafa jirgin ba. Yana bukatar injiniyoyi masu duba lafiyar jirgi, da ma’aikata masu kula da filin jirgin kafin komai ya gudana yadda ake so. To shi ma asibiti da sauran ma’aikatun lafiya haka suke. Idan babu jituwa a tsakanin wadannan ma’aikata to za a samu cikas.
Yana da kyau a gane cewa duk wannan sa-in-sa fa da ake ji kusan a kungiyance ne kawai, ba a daidaikun ma’aikata ba, wato gasar da take tsakanin ma’aikatan lafiya a kungiyance ta fi bayyana ba a tsakanin daidaiku ba. Domin idan misali likita ya ga mai bada magani a asibiti sukan gaisa har su yi shewa, ba kamar yadda wasu suka zata ba. Kusan ma wannan ya fi nunawa a tsakanin likitoci da masu jinya.  Abin da ake nufi a kungiyance shine idan kungiyar majinyata ta nemi karin albashi aka amince, ba za a dade ba za a ji kungiyar masu aiki a lab, wato dakin bincike suma suna neman kari don kawai son yin gasa da juna.
Bari mu duba su wane ne ke aiki a asibitoci. Da farko dai ya kamata masu zuwa asibiti su san cewa akwai tsari a harkar asibiti. A lokuta da dama ba likita kawai mutum ya ke zuwa asibiti gani ba, akwai masu gashin jiki wadanda ba likitoci ba ne, akwai masu daukar wani abu a jikin mutum kamar miyau ko jini don gwaji, wadanda su kuma akwai likitoci a cikinsu akwai kuma wadanda ba likitoci ba. Akwai masu daukar hotuna.
A wasu asibitoci ma’aikatan lafiya na farko da mutum zai fara gani sune masu jinya ko ungozomomi, wadanda aka yarda su ga masu kananan matsaloli, kamar na masu zuwa awo, kuma su ba su magunguna. A asibitocin sha ka tafi kuma wato dispensaries wasu ma’aikatan lafiya da ake kira Community Health Workers da ungozoma mai karbar haihuwa ake iya gani. Ba su ma da likitoci. Community Health Workers su ne wadanda aka ba horo kan kananan cututtuka da dama, kuma za su iya ba da maganinsu daidai gwargwado. Wadannan kananan matsaloli sun hada da ciwon kai da zazzabi da ciwon baya, mura da sauransu. Shi ya sa a Hausance suma ake kiransu likitoci.
Akwai kuma pharmacists wadanda muka fi sani da masu bada magani. Wadannan sun karanci hadawa da bada magani ne. Kamata yayi a ce da yawansu suna ma’aikatar sarrafa magunguna, amma da yake babu masana’antun, suna nan sun cika asibitoci. Suna da masaniya akan wasu cutuka, kuma sukan iya rubuta magani. Amma fa mafi yawa da ake gani a kyamis-kyamis dinmu na cikin gari, ba su ne pharmacists ba, su suna cikin daki can ciki sai ta baci ake ganinsu. Kamata ya yi a ce kowane kyamis akwai su, amma da dama ba a samu, don haka sai an lura sosai.
Idan aka duba har ila yau akwai ma’aikata masu bayarwa da kula da kati a asibiti, wadanda su ma makaranta suka je sukutum suka karanci aikinsu; akwai akawu-akawu masu kula da bangaren kudi, wadanda kowa ya san su ma sai sun yi karatu mai zurfi na aikinsu suke samun gurbi. Akwai masu girki, wadanda suma ba kawai mutanen gari wadanda suka iya girki ake diba ba, a’a sai mai takardar shaida. Ga masu wanki da ke aiki a laundry, wadanda ake sarrafawa da injina, wadanda su ma sai da takardar shaida suke samun aiki. Kai ga ma’aikata nan birjik tun daga masu shara har zuwa masu gadi da masu gyara filawoyi da sauransu, wadanda dole suma sai sun yi karatu a kalla na gaba da firamare kafin su samu aikin.
A manyan asibitoci, bayan nas-nas, likitan farko da za a gani a mafi yawan lokuta ana kiransa General Practitioner (GP). Wannan shi ne likita mai tantance matsala ya bada magani, idan kuma ta fi karfinsa ya turata gaba. Misali, idan da mutum zai je da ciwon kunne, to sai shi wannan GP ya duba mutum, yayi bincike, sannan ya ba da magani. Idan an ji sauki shikenan, idan kuma ba a ji sauki ba, zai iya canza magani. Idan har ila yau ba a ji sauki ba to sai ya tura mutum ya ga likitan kunne.
Amma a yayin da likitan ya fahimci cewa matsalar mutum ba karama ba ce, kuma yana bukatar kulawa ta gaggawa ko kwanciya sai ya tura shi bangaren da ake iya ganin mutum cikin hanzari (emergency), ko kuma dakin kwanciya kai tsaye, su kuma su kwantar wa wani likita da ya kware a wannan bangare. Misali, idan mutum ya zo da ciwon kirji, da haki kuma gumi na karyo masa, (alamomin bugun zuciya) sai a yi maza-maza a tura shi irin wannan wuri domin girman matsalar. Ko kuma mutum ya zo da matsalar ciwon ciki da ake kyautata zaton fashewar hanji ce, to shima dole a tura shi wurin kulawa ta gaggawa.
Akwai sauran ire-iren likitoci da masu jinya na fanni dabam-dabam. Akwai likitan fata (dermatologist) akwai na kwakwalwa mai tiyata (neurosurgeon) da marasa tiyata (neurologist), akwai kuma na ido (ophthalmologist). Likita mai lura da kunne da hanci da makogaro (Otorhinolaryngologist) duk guda daya ne. Sai mai kula da kirji (cardiothorathic surgeon) da mai kula da zuciya (cardiologist), da mai duba huhu (pulmonologist). Akwai kuma wadanda suka kware akan ciki da kayan ciki kawai (gastroenterologist), na koda ma daban ne (nephrologist). Masu yi wa mafitsara aiki, wato tun daga koda har wurin fitsari su ne urologists. Na bangaren halittun mata kuma gynaecologist. Mai kula da masu juna sunansa Obstetrician. Likitan kashi kuma orthopaedic surgeon. Likitocin da suka kware akan kiyaye al’umma kamuwa daga cutuka gaba daya kuma su ne Community Physicians, wadanda wasunsu suna asibiti, wasu suna ma’aikatu tsara harkar lafiya na hukumomi.
Ya kamata a lura cewa an rubuta likitoci da masu jinya ba likitoci kawai ba, domin su ma masu jinya suna kwarewa ne a bangarori daban-daban kamar na likitanci.
karin bayanai: Ga masu neman karin bayanai, wadanda aka tattauna a baya ko masu tambayoyi irin wadanda aka riga aka amsa a baya, bayan wannan mukalla sukan iya ziyartar sashen kundin tara bayanai na kiwon lafiya, a shafin yanar gizon a aminiya, wato http://www.dailytrust.com.ng/aminiya ko a wannan adireshi na yanar gizo lafiyarmu.wordpress.com