✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta ba Hukumar FRSC motocin sintiri

Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta ba Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa (FRSC)  motocin sintiri 21 da kuma motocin janye motocin da suka yi hadari daga…

Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta ba Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa (FRSC)  motocin sintiri 21 da kuma motocin janye motocin da suka yi hadari daga kan hanya domin shawo kan matsalar yawan aukuwar hadurra a titunan kasar nan. Ministan Ayyuka Akitek Mike Onolememen ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wurin mika makullan motocin ga Hukumar FRSC a Hedkwatar Ma’aikatar Ayyuka da ke Abuja. Ministan ya ce, gwamnati ta yanke shawarar tallafa wa hukumar ce a kokarin da take yi na rage yawan aukuwar hadarurruka a fadin kasar nan. Ministan, wanda Babban Sakatare a Ma’aikatar, Dokta Abubakar Koro Mohammed ya wakilta, ya ce gwamnati tana kokarin rage yawan aukuwar hadurra ne da akalla kashi 50 cikin 100 a fadin kasar nan. Daga nan ya hori hukumar ta yi amfani da motocin kamar yadda suka kamata. “Ya kamata ku saka wa Gwmanatin Tarayya ta hanyar kula da lafiyar motocin da kuma yin amfani da su ta hanyoyin da suka dace”, inji Ministan. A nata bangaren Hukumar FRSC ta bayyana farin cikinta a kan wannan karimci da Gwamnatin Tarayya ta yi mata.  Kuma ta yi alkawarin yin amfani da motocin ta hanyoyin da suka kamata domin ta shawo kan matsalar aukuwar hadarurruka a manyan hanyoyin kasar nan.