✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madaci ko shayi?

Wani Bazazzagin kauye ya kamu da rashin lafiya, yana ta magani tsawon lokaci bai samu sauƙi ba. Sai aka dauka aka kai shi asibiti a…

Wani Bazazzagin kauye ya kamu da rashin lafiya, yana ta magani tsawon lokaci bai samu sauƙi ba. Sai aka dauka aka kai shi asibiti a birni. Bayan an kwantar da shi a kan gado, likita ya zo da magani ya ba shi ya sha. Yana kwance a kan gado sai barci ya dauke shi, bai farka ba sai da gari ya waye. Bayan ya farka yana zaune sai aka kawo masa ruwan lipton domin ya sha. Yana fara sha sai ya ce: ’Yan birni suna jin daɗi, madacinsu ma daban ne da na ƙauye.”

Ishak Abdu Rikadawa, 08034729481