✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madallah da ayyukan alheri na Gidauniyar AZMAN

Sama da shekaru biyu da suka wuce wannan fili ya kawo wa mai karatu irin gagarumar gudunmuwar da dan kasuwar kasa da kasa a kan…

Sama da shekaru biyu da suka wuce wannan fili ya kawo wa mai karatu irin gagarumar gudunmuwar da dan kasuwar kasa da kasa a kan man fetur da iskar gas Alhaji Auwalu Abdullahi Rano da aka fi sa ni da A.A.RANO, ya bayar a lokacin, dangane da ganin habakar ilmi a makarantun Firamare da na Sakandaren Jihar Kano, kai har ma da na makwabtan jihohi. Wancan gudunmuwa ta kunshi tebura da kujeru da littattafai da sauran kayayyakin koyo da koyarwa da ba sai an fadi ba za su taimaka matuka cikin habakar ilmin `ya`yanmu da jikokinmu. Don haka ma na samu makalar taken ‘Ayi koyi da ayyukan alheri na Alhaji Auwalu Abdullahi Rano.’ 

Makalar yau din za ta mayar da hankali ne a kan irin wadancan ayyukan alheri da na ji a wani shiri mai taken ‘ALHERI DANkO’ da wasu shehunnan malaman Jami’ar Bayero da  ke Kano, wato Ferfesa Aminu Idris Tanko mataimakin shugaban jami’ar mai kula da sha’anin mulkin da Ferfesa Kabiru Isah dandago tsohon Kwamishinan kudi na Jihar Kano, kuma na sashen nazarin Akanta da Ferfesa Mustapha Isma’il na sashen harshen Larabci da kuma marubuciyar nan Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, sukan gabatar a tashar gidan Rediyo Freedom Kano a kowace ranar Lahadi da kimanin karfe 11:00 zuwa karfe 12:00 na dare a kowane mako, sannan a maimaita a cikin makon.

Kamfanin Inshorar musulinci na Nour Takaful, shi ya bullo tare da daukar nauyin shirin da aniyar a rinka fadakar da al’umma, musamman masu hannu da shuni na kasar nan, irin yadda takwarorinsu na kasashen duniya suke kafa Gidauniya don jibintar rayuwar mabukatansu walau na kusa koma na nesa da su akan dukkan abubuwan da za su tallafa wa rayuwarsu baki daya. 

A cikin haka ne masu gabatar da shirin na ‘ALHERI DANkO’ da Malam Adamu Sulaiman Muhammad na gidan Rediyo Freedom din kan jagoranci gabatarwa, yanzu sun fara zakulo irin gudunmuwar da wasu masu hannu da shuni suke bayarwa don ci gaban al’ummomin mahaifarsu da ma na kasa baki daya. Ni ma ta waccan kafar yada labarai ce na ji amon wannan shiri a lokacin da ake tattaunawa akan irin gagarumar gudunmuwar da GIDAUNIYAR AZMAN da ke karkashin jagorancin shahararren dan kasuwar nan na kasa da kasa kuma shugaban rukunin kamfanonin Azman, wato kamfanin sufuri na Azman da na hada-hadar man fetur da gas da kuma kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Azman da na fannin ayyukan gona da kiwo, wato Alhaji (Dr) Abdulmunaf Yunusa Sarina. Gidauniyar da a cikin shekarar 2017, ta kashe zunzurutun kudade har Naira kusan miliyan maitan da arba’in da bakwai (N246.85m) cikin gudanar da ayyukan da suka jibanci gina da gyaran masallatai da tallafa wa fannin ilmi da na kiwon lafiya da na matakan tsaro da ma bayar da gudunmuwa kai tsaye ga al’ummar Musulmi don su sauke farali ko sunnah da ma ciyarwa da sauran ayyukan alheri.

Ga wasu daga cikin ayyukan alherin da Gidauniyar ta Azman ta yi a shekarar da ta gabata kamar yadda na ji su ta cikin shirin ‘ALHERI DANkO.’ Bari in fara da  bangaren gina masallatai da gyaransu, Gidauniyar ta Azman ta kai dauki wajen ginawa da kawata masallacin Juma’a na kauyen Jido da ke cikin karamar Hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano da kudi N25miliyan. Ta kuma sanya shimfidun sallah na kimanin N1.5miliyan a masallacin Sheikh Muhammad Zarban da ke unguwar ‘Yankaba, dukkansu a Kano. Ta kuma gina tare da kawata masallacin juma’a na Kuje da ke babban birinin tarayya Abuja a kan kudi sama da N30miliyan. Sai yin fenti da sanya na’urar amsakuwa a masallacin Juma’a na Sarina da ke cikin karamar Hukumar Garko a kan kudi N500, 000.00k. Ta bangaren wannan fanni da ban iya kawo dukkan aikace-aikace da Gidauniyar ta yi ba, an kiyasta ta kashe sama da N75miliyan.  

Ta fannin tallafa wa ilmi Gidauniyar ta Azman ta kashe kudi da suka kai N88miliyan, wasu daga cikin ayyukan da ta yi akwai gina makarantar Islamiyya mai ajujuwa 12, da ofisoshin malamai 4, da dakunan bandaki guda 8, ta kuma kayata makarantar da kujeru da tebura da wuraren da a zauna ayi karatu a kan kudi N30miliyan. Sai gina wata makarantar Islamiyyar a kofar Nasarawa cikin birnin Kano ta lashe zunzurutun kudi har N20miliyan. Sai bugawa da raba kwafi-kwafi na Alkur’ani mai tsarki da littafin Hisnul Muslim (Larabci da Hausa) da kudinsu suka kai sama da N8miliyan. Sai buga kwafi 10,000, na Fatawoyin Aikin Hajji da Umrah da ziyara na Sheikh Abdulwahab Abdallah a kan kudi N3.2miliyan. Akwai kuma bada gudunmuwar N1miliyan da Darul Hadis da ke unguwar Tudun Yola, da wata gudunmuwar N500, 000, ga Jami’ar Yusuf Maitama Sule don gudanar da babban taronta na farko 2016/2017. Sai bayar da N5miliyan a wani asusu na jami’ar Bayero da ke Kano don tallafawa dalibai marassa galibu, don biyan kudaden karatunsu.

Ta fannin kiwon lafiya kuwa a bara, Gidauniyar ta Azman ta sai wasu naurori ga asibitin Nuhu Bamalli da ke kofar Nasarawa cikin birnin Kano a kan kudi N1.9miliyan a zaman canja wadanda ta saya shekaru 4, da suka gabata ta kuma bayar da gudunmuwar N500, 000 ga kungiyar masu gashin kashi reshen jihjar Kano, ta fannin kiwon lafiyar Gidauniyar ta Azman ta kashe N1.89miliyan. Idan mu ka koma akan fannin tsaro Gidauniyar ta Azman ta bayar da gudunmuwar N5miliyan ga ofisoshin ‘yan sanda daban-daban na Jihar Kano, tare da sayen filin makabarta a garin Garko a kan kudi N500, 000.

Akan kuma sauran ayyukan da Gidauniyar ta Azman ta gudanar a shekarar da ta gabata ta kashe N25miliyan wajen taimaka wa al’ummar Musulmi su sauke farali wato Hajji da Umrah da raba ragunan layya na kiyasin kudin da suka kai N5miliyan, da kuma ciyarwar yau da kullum da kuma ta watan azumi, da kudadensu suka kama a kan N46miliyan. Ta wannan fanni Gidauniyar ta kashe N76miliyan. Mai karatu wasu daga cikin ayyukan da Gidauniyar ta Azman ta samu aiwatarwa a a tsawon bara ke nan, kamar yadda Alhaji Sa’id Hussain Abdallah Sakataren Gidauniya ya iya tattarawa, ya mika ga wancan shiri na ‘AlHERI DANkO,’ na gidan Rediyo Freedom da ke Kano.

Koda wai, ka da mai karatu ya dauka cewa Gidauniyar  Azman, ita kadai ce Gidauniya da ta ke ayyukan alherin da suka cancanci yabo. Na tabbatar da cewa mai karatu koda a garinsu, ya san wasu masu hannu da shuni da dama da suke malala wa jama`arsu ayyukan alheri don kyautata rayuwarsu. Ga irin wadannan bayin Allah irin su Alhaji (Dr) Abdulmunaf Yunusa Sarina shugaban rukunin Kamfunan Azman, sai mu ce Allah Ya saka musu da mafificin alherinSa. Masu niyyar yin irin wadannan ayyukan, amma ba su da hali, Allah Ya yi mana budin da za mu iya bayar da ta mu gudummuwar komai kankantarta