✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai ciki

Wata mata ce haihuwa ta zo mata magashiyyan, aka dauke ta ranga-ranga sai asibiti. Likitoci suka taru bisa kanta amma ta kasa haihuwa saboda ta…

Wata mata ce haihuwa ta zo mata magashiyyan, aka dauke ta ranga-ranga sai asibiti. Likitoci suka taru bisa kanta amma ta kasa haihuwa saboda ta galabaita tun a gida, shi ya sa ba za ta iya nishi mai karfin da zai sa ta haihu ba. Ganin haka ya sa likitoci suka yanke shawarar a yi mata aiki. Babban likita ya fita ya samu mijin matar ya ce: “Matarka ba za ta iya haihuwa da kanta ba sai an yi mata aiki, domin ta galabaita, ba za ta iya nishi mai karfi ba, wanda zai sa mu samu sauki wajen ciro yaron da ke cikinta.” Mijin matar ya ce: “Likita kamar nawa ake nema

na aikin?” Likita ya ce masa Naira dubu hamsin ne ba yawa. Mijin matar ya yi shiru na dan wani lokaci, domin ko dubu goma ba ya da su. Can wata fasaha ta fado masa, ya ce wa likita: “Likita, zan iya ganin ta yanzu? Akwai maganar da zan fada mata.” Likita ya ce masa ba damuwa, ya shiga tana ciki. Ya shiga dakin da matar tasa take, ya je daidai kunnenta ya fada mata wasu kalmomi a boye, sai aka ji matar ta fara fada, tana cewa: “Lawai ka ci amanata, shekarunmu 3 da kai amma yau da rana tsaka ka yi mini haka? Allah Ya isa tsakanina da kai Lawai.” Garin fada ta manta halin da take ciki har ta haihu ba ta sani ba. Ashe ta yi nishin da ya fi wanda likitoci ke so ta yi. Bayan ta haifo da namiji zankadede lafiyayye, sai likita ya kira mijin matar ya ce masa: “Malam Lawai, wai wace kalma ka fada wa matarka ta samu karfin haihuwa? Domin mu mun yi iya yinmu ta kasa nishi mai karfi.” Malam Lawai ya yi murmushi ya ce: “Ba wani dogon labari na fada mata ba, kawai cewa na yi zan mata kishiya. Wannan ne kadai ya sa ta haihu cikin sauki. Da ban fada mata haka ba, da na yi asarar dubu hamsin.”
Daga Aliyu Basiru, 08033633835